Dakta Gumi Ga Buhari: Ka Yi Murabus Kawai, Saboda Ka Gaza — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Dakta Gumi Ga Buhari: Ka Yi Murabus Kawai, Saboda Ka Gaza

Published

on


Shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Shaikh Ahmad Mahmud Gumi, ya nemi Shugaba Buhari da ya sauka daga kujerar mulkin kasarnan, bisa zargin da ya yi ma shi na yawaitan kashe-kashe a karkashin gwamnatin na shi.

A lokacin da yake bayanin hakan lokacin da yake gabatar da karatun tafsirinsa na watan Ramadan, Malamin na Musulunci ya sha sukan gwamnatin ta Buhari inda yake kwatanta ta da tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan.

Ya bayar da misalin kiran da ya yi wa tsohon Shugaba Jonathan da ya sauka a daidai lokacin da kashe-kashen Boko Haram ya tsananta. Domin jinainai sun yawaita a hannunsa,” Shaikh Gumi wanda ya daga wa masu sauraronsa shafin gaba na jardar, New Nigerian, domin nuna masu shaidan inda ya soki tsohuwar gwamnatin ta Jonathan.

“Ina zargin gwamnatin ta Jonathan ne, sabili da jini ya yawaita a hannunsa, Boko Haram suna sanya bamaibamai a ko’ina ba tare da gwamnati ta yi wani abin a zo a gani ba.

“Duk wanda aka kashe a karkashin mulkinka, jininsa na kanka ne. in har ka yi abin da ya dace, zan iya cewa, Allah na iya gafarta maka. Amma in har ka yi sakaci, sam ba yanda Allah zai gafarta maka. To yanzun ma lamarin duk daya ne da na baya.

“Zubar da jinin ma da ake yi a halin yanzun har ya ma fi na bakidayan zamanin mulkin Jonathan.

“Yanzun sai ku yi wa kanku adalci, domin Addininmu na adalci ne.

“A mulkin Jonathan da jini ke ta kwarara da yawa, a Masallatai, Cocina da layuka, cewa na yi ya kamata ya sauka, saboda na ga baya iya magance kwarararn jinanan. Ba zai iya ba. Sai na roke shi da ya sauka nan take, saboda ka kasa magance kashe bayin Allah da ake ta yi ba gaira ba sabar.

“Don haka ne na yi kiran da ya sauka, an kuma buga hakan cikin jaridu duka, me zai hana da a yi hakan a yanzun?

“Yanzun jinin ma da ke kwarara ya fi na wancan lokacin yawa saboda sakaci, da rashin nuna damuwa,” in ji shi.

A cewar shi, “Rashin damuwa shi ne, a lokacin da ake ta kashe bayin Allah a cikin kasa, sai Shugaban kasa da gwamnonin shi suka zabi su ta fi wajen shagulgulan buki.

“A irin wannan halin, ta ya zaka ta fi wajen wani shagalin buki.

“Idan dai har zan yi wa kaina adalci, kamar yadda a wancan lokacin na kirayi Jonathan da ya sauka, yanzun ma ya kamata na kirayi Buhari da ya hanzarta ajiye mulkin kasa ba tare da wani bata lokaci ba! Yanzun ma ya kamata jaridun gwamnati duk su dauki wannan kiran nawa, in dai har gaskiya ake nufi.

“Duk da lalacewar Jonathan, ya fi zama mabiyin dimokuradiyya domin shi ya baiwa mutane ‘yancinsu na fadin albarkacin bakin su, ko da kuwa sukansa suke yi. Kuna iya gani da ya hangi akwai matsala, sai ya ajiye mulkin, yana mai cewa, ba ya bukatar ana zubar da jinainai.

“Wannan mutumin (Jonathan), ya gina mana Jami’o’i tara a Arewa, da sama da makarantun almajirai 150. Hatta wannan titin Jirgin kasan na tsakanin Abuja da Kaduna, duk aikin Jonathan ne, ya yi mana abubuwa masu yawa. Amma duk da hakan na yi kiransa da ya sauka saboda kwararan jinainai….domin jini ya fi komai tsada a rayuwa.

“Ba irin abin da ban fada ba a kan gwamnatin ta Jonathan. Har cewa na yi a tsige shi, na ce ya sauka, shi dan rigima ne…

“Amma yanzun ina da zabi daya ko biyu. Idan har a matsayinka na dan’uwana ba zan iya gaya maka abin da na gaya wa wancan mutumin ba, to ya kamata na tafi Abuja na shiga Jirgin sama na tafi wurin Jonathan na roki da ya yafe mani kiran da na yi ta yi masa a cikin mutane kan hakan.

“Ko dai na tafi neman yafiyan Jonathan, ko kuma shi ma wannan na yi masa kiran da na yi wa Jonathan din, ba wata hanya ta uku kuma.

“Hakurinmu ya isa da wannan gwamnatin. Idan da wata ce ba ita ba, wallahi da ba za mu yi hakan ba.

“Mutane sai mutuwa suke ta yi a kullum. Ko a jiya an sace wani. Mutane suna cikin bakar wahala, kuma babu mai fadin hakan, saboda duk sun makure mana wuya don ba sa son jin an fadi wata magana marar dadi a kansu. Wannan Masallacin Tauhidi ne. hakan ma ya isa dalilin da zai sa a gaya wa mutane gaskiya.

“A lokacin da mutane suke cewa, Yesu Allah ne, sai Allah Ya saukar da aya, ta kaskantar da Yesun, ba domin komai ba sai domin ya nuna masu cewa, in Allah din Ya so, zai iya halakar ma da shi bakidaya.”

Malamin ya ce, a lokacin da mutane suke kokarin daukaka matsayin wani dan adam zuwa matsayin da ba na shi ba, sai a sanya mutumin ya nuna wa mutane cewa shi fa dan adam ne.

“Buhari yana aikata kurakurai da yawa. Kurakurai masu yawa kuwa! Kuma shi mutum ne kamar kowa. Ina maku rantsuwa da Allah, akwai mutane masu yawa a Arewacin kasarnan da za su iya aikin da ya fi na Buhari matukan gaske.”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!