Yaya Taure Ya Yi Min Karya -Guardiola — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Yaya Taure Ya Yi Min Karya -Guardiola

Published

on


Mai koyar da tawagar yan wasan Manchester City Pep Guardiola ya bayyana cewa tsohon dan wasan kungiyar, Yaya Taure, makaryacine bayan dan wasan ya zargi Guardiola da cewa yana nunawa bakaken yan kwallo banbanci a kungiyar.

A makonni biyu da suka gabata ne dai Taure yayi wata hira da wani gidan talabijin a kasar Faransa inda ya bayyana cewa Guardiola bayason bakaken fata kuma yan ayawan nuna banbanci idan ya tashi yanke wani hukunci a kungiyar.

Sai dai a satin daya gabata dan wasan tsakiyar kungiyar, Kebin De Bruyne ya karyata Yaya Taure inda ya ce karya kawai yayiwa Guardiola saboda hakan ba halin mai koyarwar bane sai dai idan shine yake tunanin haka.

“Karya kawai yayi min saboda gaba daya zancensa babu kamshin gaskiya aciki sai son zuciya kuma shekarar mu biyu dashi a City amma bai taba tareni ya gayamin ba sai bayan yabar kungiyar yaje yana gayawa mutane” in ji Guardiola

Yaya Taure dai yabar Manchester City a karshen kakar data gabata kuma yana dab da komawa kungiyar Westham United kungiyar da tsohon kociyan Manchester City yake wato Manuel Pellegrini.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!