Za Mu Hargitsa Fadar Shugaban Kasa Matukar Aka Taba Obasanjo –ADC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Za Mu Hargitsa Fadar Shugaban Kasa Matukar Aka Taba Obasanjo –ADC

Published

on


Jam’iyyar ADC, wacce tsohon Shugaban kasa, Obasanjo ya ke yiwa jagoranci, ta gargadi gwamnatin tarayya da cewa, matukar suka kai ga taba Obasanjo din, to su kuwa za su hargitsa fadar Shugaban Kasa ‘Aso Rock’.

Shugaban Jam’iyyar na kasa, Cif Okey Nwosu, ne ya fadi hakan cikin wata tattaunawa ta waya da suka yi da manema labarai a ranar Juma’ar da ta gabata.

Nwosu ya ce, gazawar da Jam’iyyar APC ta yi na kasa cika alkawurran da ta yi wa al’umma ne ya sanya gwamnatin Buharin ta koma kame-kamen kulla wa abokanan adawanta.

Nwosu ya ce, a lokacin da Obasanjo yake tallafa wa rundunar kamfen din Buhari a shekarar 2015, sunan da Buhari da magoya bayansa ke kiran Obasanjo da shi, shi ne ‘Jagoran kawo sauyi,’ amma sai ga shi a yau wai ana zargin wannan mutumin da sunan mai laifi, saboda kawai yana yayata laifin gwamnati.

“Bai yiwuwa ku taba Obasanjo. A shekarar 2014 da 2015, shi ne kuke kira da, ‘Jagoran kawo canji,’ saboda yanayin da kuke ciki a wancan lokacin, shi kuke dagawa a matsayin gwarzon ku na samar da sabuwar Nijeriya.

“Amma yanzun da lamurra suka lalace a sassan tsaro da tattalin arziki, ya fito yana gaya maku gaskiya, sai ga shi kuna neman kama gwarzon samar da sabuwar Nijeriyan da kuke fada. to mu kuwa zamu tuntudo dukkanin ‘yan Nijeriya, da su mamaye fadar Aso, matukar gwamnati ta takale mu.”

Sai dai, wasu kungiyoyi biyu, ‘Socio-Economic Rights’ da ta ‘Accountability Project and the Committee for the Defence of Human Rights,’  kira suke da cewa, lallai sai Obasanjo ya shirya fuskantar tuhuma matukar dai aka iya tabbatar da shaidun aikata cuwa-cuwa a tsohuwar gwamnatin na shi.

Daraktan na kungiyar ta SERAP,  Adetokunbo Mumuni, cewa ya yi, ankararwar da Obasanjo ya yi na cewa Shugaba Buhari na yi ma shi bita da kulli, ba shi da wata fa’ida, domin ya zama tilas ga hukumomin hana aikata laifukan karya tattalin arziki  da su gudanar da ayyukan su.

Mumini ya ce, “Gaskiyan magana shi ne, ba Buhari ne ya kamata ya sanya hukumar EFCC kan wani ba, hukumomin tsaron ne ya kamata su yi aikinsu da kansu, na bincikar kowane irin zargi, da kuma aikata laifi, kan ko ma waye. Wannan kukan na Obasanjo ba zai hana su gudanar da aikin su ba, matukar dai akwai wasu shaidun aikata laifi a kansa.

Shi ma shugaban kungiyar kare hakki ta, CDHR, Malachy Ugwummadu, cewa ya yi, bai kamata Obasanjo ya fito yana wannan kukan ba. Ni ina ganin babban ci gaba ne matukar wannan gwamnatin tana ganin tana da karfin ja da Obasanjo din.

“In gwamnatin tana da tabbatattun bayanai ko shaidu da za ta iya ja da Obasanjo, hakan ya nuna dukkanin mutanan da suka shugabanci kasarnan tare da shi ma ana iya tunkararsu.”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!