AMCON Ta Karbo Naira Biliyan 740 Daga Wadanda Ake Bi Bashi A 2017 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

AMCON Ta Karbo Naira Biliyan 740 Daga Wadanda Ake Bi Bashi A 2017

Published

on


Manajin Darakta na hukumar kula da kadara ta kasa (AMCON), Alhaji Ahmed Kuru ya sanar da cewar, hukumar ta karbo basussukan da ake bi na naira biliyan 740 a shekarar 2017.

Ahmed ya sanar da hakan ne a ranar juma’ar data gabata a taron manema labarai da hukumar ta kirawo a jihar Legas.

A cewar sa, kwarai muna kadarori da dama wadanda suka hada da gidaje da kuma wasu sauran kadarori kuma babban mahimmanci shine, an samu nasarori da dama duk a cikin wannan lokacin.

A cewar sa, hukumar ta samu nasarar karbo kimanin kashi talatin da bakwai bisa dari  da ya kamata ta karbo.

Ya kara da cewa, a bangaren kamfanoni hukumar ta kuma samu nasarar karbo kashi kimanin kashi hamsin bisa dari.

A cewar sa, idan kuka kwatan ta da yadda abin yake wanda ya kai kamar a fadin duniya, mun yi namijin kokari sosai.

Kuru ya kara da cewar, duk a tsakanin lokacin hukumar ta karbo wasu kadarori harda na bankuna uku kuma tana kan hanya akan na kamfanin hada motoci kirar PAN.

Ya yi nuni da cewar, wannan ya hada da kari da wasu matsakaitun kasuwanci da muka samar da dauki.

Ya ce, daukin da muka bayar akan aikin noma a yankin ya kai na kimanin naira tiriliyan 1.7 da kuma fannin kasuwanci.

Sai dai, Kuru ya koka akan duk da wannan daukin da hukumar ta yi akan fannin kasuwancin da kuma irin kudin data zuba a baya kakarin da aka yi bai kai na azo a gani ba, inda bai wuce kashi goma bisa dari ba.

Ya sanar da cewar, asarar hukumar ta ragu daga naira biliyan 164.94 a shekarar 2016 zuwa naira biliyan 16.41 a shekarar 2017.

Kuri ya sanar da cewar, kamar yadda aka sani ne, hukumar ba wai an kafa ta ne don tara riba ba kuma hukumar ta yi iya kokarin ta wajen cimma burin dalilin da ya sanya aka kafa ta, musamman wajen samar da daidaito akan harkar tara kudi.

Ya ce, idan tattalin arzikin yana tafiya kamar yadda ya kamata, wasu daga cikin kasuwancin komai zai tafi daidai in kuma an samu akasin hakan, kasuwancin shima zai fuskanci matsala.

Kuru ya yi nuni da cewar, muna gudanar da kyakywan shiri akan gidajen saboda yadda yanayin tattalin arziki ya canza, domin idan muka sayar dasu a yau, zamu yi babbar asara.

A cewar sa, a lokacin da tattalin arzikin ya fara mikewa, fanin kasuwancin gidajen sai ya fara habaka wanda a lokacin zamu iya sayarwa, in kuma muka sayar dasu a yanzu, baza mu iya samun riba ba.

Ya sanar da cewar, hukumar tana gudanar da aiki kafada da kafada sashen shari’a da ‘yan majalisa don yin nazari akan dokar data kafa hukumar yadda za’a yi mata kwakwarima don inganta ayyukan ta.

Kuru ya sanar da cewar, majalisar kasa ta jima tana bayar da goyon baya  kuma muna kokarin samar da kotu ta musamman, inda wasu manyan alkalan kotuna da suke da kima don duba kararrakin mu cikin sauri.

A cewar sa, “a yanzu mun yanke shawarar samar da canji da kuma dabarun mu akan karbo kadarori, inda ya ce, a yanzu mun karbo kadarorin. Zamu kuma samu wasu masu saye na daban, ma’ana mutanen da za su iya saye.

A karshe ya ce, hukumar tana tunkarar shekarar 2023 don sanya ayyukan ta da kuma yin alkawari wajen kara zage damtse don karbo sauran kadarorin kafin ranar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai