Ba Za A Sake Yin Magudin Zabe A Nijeriya Ba -Jami’in INEC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ba Za A Sake Yin Magudin Zabe A Nijeriya Ba -Jami’in INEC

Published

on


Cikin makon jiya ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa magudi a lokacin zabe ba abu mai sake yiwuwa a Najeriya ba. Daya daga cikin manyan jami’an INEC din ne ya bayyana haka a lokaci guda kuma ya na karyata zargin da wasu ke yi cewa hukumar zaben wai ta na mara wa Gwamnatin Tarayya baya.

Ya buga misalai da wasu zabuka da dama wadanda INEC ta gudanar a cikin shekaru uku din nan, wadanda ya ce jam’iyyar adawa ce, musamman ma PDP ko wata jam’iyya daban ce ta yi nasara a kai, ba jam’iyya mai mulki ba.

Majiyar ta ci gaba da yin watsi da wani zargin da ake yi wai jam’iyyar APC da kuma gwamnati na shirye-shiryen yin magudi a zaben 2019. Daga nan sai ya ce ai fasahar zamani da INEC ta shigo da ita, ta bai wa masu zabe damar zaben wanda ran su ke so, ba tare da yi musu katsalandan ko ta wace hanya ba.

Ya kuma tabbatar da cewa na’urar ‘card reader’ wadda ta tabbatar da sahihin zabe tun a 2015, a wannan lokacin ma za a yi amfani da ita a kusan runfuna dubu talatin na fadin tarayyar kasar nan a zabe mai zuwa. Wannan kuwa kamar yadda ya yi karin bayani, abu ne da zai haka duk wata hanyar yin murdiya ga zabe.

Daga nan kuma ya kara da cewa ba za a kirkiro wasu sabbin rumfunan zabe kafin babban zaben 2015 ba. Ya ce idan ka kirkiro runfunan zabe, tilas sai ka na da wadanda za su yi zabe a wurin. Yin hakan kuwa, inji shi, zai harfar da rudani.

“Abin da INEC kawai za ta yi, shi ne a kirkiro wasu mazabu a cikin mazabun da a ke da su, amma a inda masu zabe a mazabun su ka haura mutum 500,” in ji shi, wanda ya kara da cewa, “a lokacin Farfesa Attahiru Jega, INEC ta kirkiro rumfunan zabe har a cikin wuraren bautar da a ka fi sani da ‘shrines’ da wasu wurare daban. Amma daga tantancewar da mu mu ka yi, a yanzu mu na da rumfuna 119,973 a fadin kasar nan. Kuma babu sauran wata rumfar zabe da ke cikin wani wuri da za a gani ko a ji bambarakwai.”

Daga karshe ya ce, yanzu ne lokacin da ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa za su hada kai da jami’an zabe, domin kara inganta sahihancin INEC, domin zama kyakkyawan misali ga kasashen Afrika.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!