Ba Za Mu Amince Da Yunkurin Bata Wa Dogara Suna Ba, Inji Aminu Tukur — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Ba Za Mu Amince Da Yunkurin Bata Wa Dogara Suna Ba, Inji Aminu Tukur

Published

on


A jiya ne ‘yan tawagar tafiyar siyasar Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara suka

bayyana bacin ransu dangane da yunkurin shugabanin APC a kananan hukumomin Bagoro, Dass da Tafawa Balewa suke yi na cewa suna gargadin Dogara kan batun sanya hanu a yunkurin tsige Buhari.

Sun mayar da martanin ne a ganawarsu da manema labaru a sakatariyarsu da ke Bauchi jiya, inda Muhammad Aminu Tukur wanda kuma dan majalisa ne da ke wakiltar mazabar Lere/Bula a majalisar jihar Bauchi, ya bayyana cewar an yi amfani da wannan damar ne wajen cimma manufar da ke boye na yunkurin bata wa Kakakin Majalisar Tarayya suna.

Tun da fari ma, Aminu Tukur ya yi tsokaci dangane da wadanda suka shelanta cewar sune zababbun shugabanin APC a kananan hukumomin uku, yana mai shaida cewar an yi munamuna a lokacin zaben wanda yanzu haka suna ma kotu tare da su kan zaben da aka kitsa aka ce sune jagororin APC.

Ya ce; “Ni zababben dan majalisa ne, idan magana za a yi da sunan mutanen wannan yankin da ni da Hajiya Maryam Garba Bagel muna ya fi cancanta a ce mu yi magana idan da gaske ne sun yi magana ne da yawun mutanen wannan yankin, kawai tsararren lamarin ne domin a bata wa mai gidanmu suna wanda kuma ba za su lamunci hakan ba,” In ji shi.

Ya bayyana cewar daga cikin wadanda suke yunkurin bata wa Dogara suna akwai wanda suke ganin bai taba son Buhari ba, kuma bai taba zabensa ba, “Shi Malam Haruna Rikaya wanda ya kasance zababben shugaban APC a karamar hukumar Bogoro kafin wa’adinsu ya kare, wanda kuma aka sake nadasa a zaben 2018, za mu yi masa alfahari cewar idan akwai wadanda suka yi wa Buhari hidima a jihar Bauchi muna ciki.

Aminu Tukur ya bayyana cewar a zaben 2015 da ya gudana Haruna Rikaya bai zabi shugaban kasa Muhamadu Buhari ba, don haka sharri ne kawai suke yi wa Dogara.

“A lokacin da aka zo tafiyar APC Dogara duk inda ake zancen tara kudi Yakubu Dogara yafi kowa bayar da adadi mai tsoka na kudi domin ganin Buhari ya samu nasara a jihar Bauchi,”

Ya ci gaba da bayyana irin gudunmawar da Dogara ya baiwa Buhari a lokacin yakin neman zabe; “Dogara shine wakilin akwatin Buhari a lokacin zaben da ya gudana a birnin Legas, a wannan ranar Malam Haruna Rikaya da na ke fada wallahi bai zabi Buhari ba, Rochas Okorocha ya zaba.

Ya kara da cewa; “Dogara ya fada ya ce idan ba za ka zabi Buhari ba kada ka zabeni,” In ji Aminu Tukur.

Dangane da zargin da mutanen suka yi wa Dogara kuwa, Muhammad Aminu Tukur ya shaida cewar ‘yan majalisu suna gudanar da aikinsu ne yadda ya dace, don haka bai kamata wani wanda ba kowa ba yake tsoma musu baki a cikin aikinsa wanda dokace ta basu ba; “Sun yi aikinsu kamar yadda doka ta basu, suka ce masa gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba. don sun yi aikinsu sai ya zama laifi? Yau idan da dukkanin gwamnonin kasar nan za su ce Buhari kai mutumin banza ne zai kaisu kotu wallahi duk a daure su. Amma idan dan majalisa daya ya tashi ya ce Buhari kai mutumin banzane babu wanda ya isa ya ce mishi kala, saboda shi ne ke da hurumi a kansa,”

Bai tsaya haka ba, ya ci gaba da wanke mai gidansu; “Sannan ya kamata a gane, shi mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari ba a taba samun wani zaure da taba zaunawa ya ce Dokara kai mutumin banza ne. shugaban kasa ya sha fada kan cewa Dogara ne alamin matasa masu tasowa da za su jagoranci kasar nan bisa gaskiya da cancanta,” In ji Tukur.

Aminu Tukur ya bayyana cewar a Dogara ya yi yaki sosai wajen kare wa Buhari martaba, yana mai shaida cewar bai kamata ko da wasa wani ya zo yana cewa Dogara bai son Buhari.

“Abun da muka sani mai girma Kakakin Majalisar Tarayya mutum ne mai daraja shine na hudu a dukkanin Nijeriyar nan, kuma yana da dukkanin mutuncin da ya dace a kare masa akan ababen da suka jibinci gaskiya,” In ji Shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Dan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben da ke tafe, Kaftin Bala Jibrin ya yi zargin cewar gwamnan jihar Bauchi mai ci bai taba son Buhari ba a lokutan da aka yi ta yakin neman zabe har ma daga bayan zaben.

Ya shaida cewa gwamnan ya fi son Obasanjo da Atiku akan Buhari don haka ne ya shaida cewar wannan matakin da gwamnatin ta dauka na bata wa Dogara suna ba zai kai ga gaci ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai