Buhari, Osinbajo Da Tinubu Sun Gaza Biyan Kudin Harajin Jam’iyya, Inji APC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Buhari, Osinbajo Da Tinubu Sun Gaza Biyan Kudin Harajin Jam’iyya, Inji APC

Published

on


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mataimakinsa Yemi Osinbajo da dukkanin ‘ya’yan Jam’iyyar APC, ba su biya kudin Harajin Jam’iyyar ba a shekarar 2015. Jam’iyyar ta APC ne ta fadi hakan a rahoton ta na kudaden da suka shigo wa Jam’iyyar a cikin shekarar.

Jam’iyyar ta ce, ba ma su ba, kaf ‘ya’yan nata a duk fadin kasarnan, ba wanda ya biya hakkin da ya hau kansa na Jam’iyyar a shekarar zaben ta 2015, hakan ne kuma ya jefa ayar tambayar, to ta ina Jam’iyyar ta sami kudaden da ta gabatar da aikace-aikacenta a wannan shekarar zaben ta 2015.?

Babu dai tahakikanin yawan ‘ya’yan Jam’iyyar ta APC da ke fadin kasarnan, amma dai wasu jami’an Jam’iyyar na misalta yawan ‘ya’yan Jam’iyyar a sama da milyan guda.

A wata-wata ne wasu lokutan kuma a shekara-shekara ake neman ‘ya’yan Jam’iyya da su biya kudaden Haraji na Jam’iyya, wanda hakan ne babban hanyar da Jam’iyyu ke samun kudaden ayyukansu. A bisa zahirin gaskiya ma, Jam’iyyar ta APC ta tara Naira milyan 23.7 a shekarar 2014.

Amma sai ga shi Jam’iyyar na cewa ko mutum guda bai biya hakkin Jam’iyyar ba a shekarar 2015, ciki kuwa har da Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo, wannan batu ne da manazarta suke tababan gaskiyan da ke cikin sa, wanda ya saka wani shakkun a kan rahoton na masu binciken kudin Jam’iyyar.

Wani manazarcin ma cewa yake yi, Jam’iyyar ta APC wacce ke da’awar yakan cin hanci da rashawa, kila ma dai ta dogara ne kan sununun kudin da wasu da suka yayibo suke zuwa su jibge mata, a maimakon kudaden halas wanda ‘ya’yan Jam’iyyar kan biya na Haraji.

“Gaskiya hakan ya nuna akwai matsala, ko dai masu binciken ba su bincika da kyau ba, ko kuma kwamitin binciken akwai matsala a cikinsa,” in ji Eze Onyekpere, shugaban cibiyar adalci, wacce kungiya ce mai lura da kudaden kamfen da Jam’iyyu ke kashewa.

“Wannan ya nuna Jam’iyyar ba ta damu da kananan kudaden da take tarawa ba, ta dogara ne a kan masu kawo mata makudai. Duk kuwa wanda zai zuba maka makudai yana sa ran ya girbi riba ne. hakan kuma shi ke kawo cin hanci da rashawa.”

Jam’iyyar ta APC ne dai ta hannanta wa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, wannan rahoton nata kamar yadda doka ta tanada, inda kafar yada labarai ta, ‘PREMIUM TIMES,’ ta yi tsinkayar sa.

Rahoton Jam’iyyar ya nuna cewa a shekarar ta 2015, ta tara kudadenta ne daga sayar da takardun neman tsayawa takara, “gudummawa da kuma kyaututtukan da ta samu.” Ta ce ta sayar da takardun neman shiga takara na Naira milyan 329.4, ta kuma samu gudummawa da kyautukan Naira milyan 275.

Shugabannin Jam’iyyar da dama da aka tuntuba sun ki cewa uffan kan wannan batu.

Sakataren yada labaran Jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, lokacin da muka tuntube shi kan wannan rahoton sai ya mika mu ga babban mai bincikar kudaden Jam’iyyar na kasa.

Shi kuma da muka yi magana da shi ta waya, mai binciken kudin, Geoge Moghalu,  sai sai ya ce sai dai mu hadu ido da ido, haduwar namu da ba ta yiwu ba da shi kenan har lokacin hada wannan rahoton.

Babban ma’ajin Jam’iyyar na kasa, Bala Mohammed, ya shaida wa, ‘PREMIUM TIMES,’ cewa, ya zuwa shekarar 2015, Jam’iyyar ba ta fara, ‘moran kudaden da ‘ya’yan nata ke biya ba.’ Amma ya kasa bayyana yadda kuma aka yi ta iya moran kudadan ‘ya’yan nata a shekarar 2014.

“Dukkanin ‘ya’yan Jam’iyya suna biyan kudin Haraji ne a kowane wata na Naira 100. Zababbun jami’ai kuma tun daga kan Shugaban kasa, ‘Yan Majalisu, Ministoci, Nade-naden siyasa, kamar shugabannin hukumomin gwamnati, wakilan hukumomin da gwamnoni, duk suna biyan wasu harajai na musamman da ya hau kansu.

“Biyan wadannan hakkoki ne ke cancantar da duk dan Jam’iyya ya mori duk wata alfarma ta Jam’iyya.

“A shekarar 2015 ba mu fara ne ba. Yanzun ne muke kokarin farawa, saboda mun fuskanci matsaaloli da yawa daga masu kamfanonin waya. Har yanzun dai ba mu kai ga cimma matsayar karshe ba da su. Saboda zai fi sauki a iya zabtare Naira 100 daya din daga wayar mutum, a duk inda yake matukar dai akwai waya a wajen.

“A gaskiya ba a biya ko sisi ba a 2015, don haka muka nemi jami’anmu da su biya har da na baya da ba su biya ba a halin yanzun. Wakilan Majalisar Wakilai na kasa sun ki yarda su biya na shekarar 2015 din, amma wakilan Majalisar Dattawa su sun amince da su biya. Amma ba a shigar da hakan ne ba a cikin rahoton ballantana a tantance da ko wanne ne na shekarar 2016 da kuma na bayan, watau 2015,” in ji shi.

Sai dai, Bala Mohammed, din shi ma ya kasa bayyana yadda Jam’iyyar ta APC ta iya tara Naira milyan 20 a shekarar 2014 daga kudaden da aka ce ‘ya’yan Jam’iyyar sun biya, duk da ya ce ba su fara karba ba har zuwa shekarar 2015.

Domin kokarin sanin ko ‘ya’yan Jam’iyyar sun biya kudaden Harajin a shekarar da ake magana a kai, wakilinmu ya tuntubi wasu daga cikin shugabannin Jam’iyyar.

Tunde Rahman, kakakin jagoran Jam’iyyar, Bola Tinubu, da muka tuntube shi sai ya umurce mu da mu tuntubi Jam’iyyar.

Garba Shehu, Kakakin Shugaban kasa, bai amsa duk kiran da muka yi masa ba, bai kuma maido mana da sakonnin da muka aika masa ba ta wayoyinmu, hakanan gwamnan Jihar Kaduna, el-Rufa’i.

Shi kuwa babban daraktan kafar yada labarai ta kasa, Muryar Nijeriya, wanda kusa ne a Jam’iyyar ta APC, Osita Okechukwu, cewa ya yi, ‘Ba zan iya tuna lokacin da na biya irin wadannan kudaden ba ga Jam’iyyar.”

 

Advertisement
Click to comment

labarai