Cikakken Mutum (I) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

Cikakken Mutum (I)

Published

on


dahiraliyualiyu@gmail.com                    +2349039128220 (Tes Kawai)

Waye a cikinmu ba ya son zama cikakken mutum? Dukkaninmu muna so mu zama mutane masu hikima, hankali, kwarjini da basira. Tamkar dai mutum din da masana falsafa suka kira  “Al-insanil Kamil”, Friedrich Nietschez (1844-1900 AD) ya kira da “Super man”, Aristotle (384-322 BC) ya kira da “idle man”, Confucius ( 551-479 BC) ya kira da mutum mai cikakkiyar falala, Gotama Buddha (480-400) ya tabbatar ya hau matsayin “Nirbana”, Ibn Sina ya kira da mutum na hakika (Al-insanil Hakiki), Jalaludden Rumi ya kira da kebantattun Allah (khawasul Allah), Emel Durkheim ya kira da “Homo-dupled” kuma shi ne dai abinda wasu sufayen suka kira da “kudubi”.

Dukkaninmu muna burin wata rana a ce mun zamo masu tunanin da babu kamarsu. Mu zamo kamar Gazzhali, Ibn Rushed, Razi, Jabir bn Hayyan, Albert Einstein, Richard Feynman ko Stephen Hawking. Babu wanda zai gayamaka cewar ba ya son ya zama kamar wadannan sai wanda bai san su waye wadannan ba. Duk wani tunanin masu tunani akan su zama kamar wadannan suke ko su debo wani sashi na wadannan mutane.

Kowa yana so ya zama mai nutsuwar zuciya kuma wayayye lamba ta farko ta fuskar addini, rayuwa, siyasa da zamantakewa. Abin damuwar shi ne ba kowa kuma ya shirya ya zama hakan ba. Abu ne mai sauki ka ga kowa yana fatan ya samu canji amma kuma mai wuya ya dabbaka abinda zai sa ya samu canjin. Waye a cikinmu bai taba cewa idan sabuwar shekara tazo zai canja ba? Shin burace-buracenmu sun iya canja rayuwarmu? A cikin kowane canji ana bukatar shiri na musamman domin samun nasara.

Rayuwarmu a kewaye take da sarkoki da suke hanamu canja tunani. Tsoron abinda muka gada daga iyalinmu, muke gani a makotanmu, muka saba da shi a kabilarmu, muke rike da shi a kungiyoyinmu, da wanda muke gani a gun mutanen da suke kewaye damu. Kadan daga cikinmu suke iya fita daga dabaibayin da suke ciki na tsoron mai zai iya faruwa da su don su canja. Idan kana so ka gane wa yake bautar da kai to ka duba ka ga waye na kusa da kai da idan ya yi kuskure ba zaka iya gyaramasa ba? Wa kake yi wa biyayya a komai baka taba ganin kuskurensa ba? Wanda yake son zama cikakken mutum sai ya fara gane yana da babbar matsala a kewaye da shi.

Har yanzu asalin tarihinmu tun muna zaune da dabbobi da irin tsarin tadawwurin da muka samu a kogo (cabe men) yana tare damu. Ka yi tunanin mutumin da yake tsakanin namin daji da suke farautarsa kamar zaki da damisa. Ka yi tunanin wace irin rayuwa zai yi. A matakin farko zai zamo mai tsoron canjawa ko motsawa daga inda yake don kada su kawomasa harin da zai kashe rayuwarsa. Har yanzu muna tare da wannan duk da muna zaune acikin duniyar da ganin zaki sai mutum ya tafi gandun dabbobi. Tsoro ne yake tafiyar damu har mu kasa canja abinda ya kamata mu canja a rayuwarmu.

Kafin mutum ya zama cikakke sai ya bi ta wasu matakai a rayuwarsa. Mataki na farko ana kiransa da “Pre-conformism”, lokacin mutum yana yaro karami bai san ya kwaikwayi wani abu agun wani ba. Yaro yana dariya akan abinda jama’ar gari suke ganin ba abin dariya bane, ya yi kuka a lokacin da ya ga dama kuma  ya aikata abinda yake so ba tare da ya kalli me na kusa da shi suke aikatawa ba. Wannan shi ne yancin da mutum yake fara samu a lokacin da babu takalidanci ko makauniyar biyayya ga kowa. Wannan yancin masana falsafa suke burin samu bayan fahimtar kansu. Suna son samun yancin aikata abinda suke da bukata ba tare da la’akari da na kusa da su ba. Su fadi gaskiya ga duk wanda ya dace su fadawa ta hanyar da ake yi wa yaro kirari da cewa “yaro ba ya karya”.

Mataki na gaba da mutum ke shiga shi ne lokacin biyayya ido rufe. Lokacin kwaikwayo mara dalili. Mutum yana fara kwaikwayar abinda ya gani ana yi a gidansu, sai makotansu, sannan a makarantu da sauran guraren da yake cudanya da su. A wannan lokacin, ra’ayin wasu shi ne ra’ayinsa, tunanin wasu shi ne tunaninsa, biyayyar wasu ita ce biyayyarsa. Mutane dayawa suna zama acikin wannan yanayi har tsawon girmansu. Dayawa ba sa tunani kuma suna tsoron sabawa da abinda suka tashi suka ga ana yi ko da kuskure ne. Irin wannan mataki ake kira da “conformist stage”.

Mataki na uku kuwa shi ne matakin da mutum ya samu yancin kansa kuma yake amfani da hankalinsa ba tare da ya dogara da wasu ba. Dogaronsa ga wasu zai zamo wajen amfani da iliminsu ne amma ba wajen yi musu biyayya ido rufe ba. Mutumin da yake a wannan mataki shi ne yake iya kawo ci gaba a duniya ta hanyar tunani, sabon ilimi da kuma amfani da hankali. Mafi yawan masana Falsafa a wannan bangaren suke. Suna tunanin kawo abinda ake ganin ba zai yi wu a kawo ba ko samar da abinda ake ganin ba zai taba yiwuwa a samar da shi ba. Wadanda aka sani da juyin-juya-halin ilimi da ci gaba, kamar Sir Issac Newton, Albert Einstein, Richard Feynman da sauransu, duk suna kan wannan mataki ne. A masana daga musulmi ko larabawa akwai irin su Ibn Sina, Alfarabi, Ibn Rushd, Algazhali da sauransu, duk suna kan wannan mataki ne. A matakin ake iya samar da ci gaba kuma a canja tunani domin samar da kyakkyawar nasara. Wannan mataki ake kira da “post conformism”.

To ko yaya mutum zai iya canja tunani ya tashi daga mataki na biyu (conformist stage) ya koma mataki na uku (post conformist stage)? Ta yaya mutum zai iya zama cikakken mutum (ko wani abu makamancinsa)? Ta yaya mutum zai kawo canjin da al’umma za ta karba kuma a samu kyakkyawar nasara? Me za mu iya yi don nasarar rayuwarmu da wadanda suke kusa da mu? Wace hanya ce za mu bi don mu zama cikakku kuma wayayyun mutane? Ya zamu fita daga sarkar da ta dabaibaye mu take hanamu ci gaban rayuwa a daidaiku ko a jama’a?

 

Wannan sai a rubutu na gaba…

 

Advertisement
Click to comment

labarai