Cikasoron Minna Ya Zama Gado Da Masun Bargu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Cikasoron Minna Ya Zama Gado Da Masun Bargu

Published

on


Mai martaba sarkin Bargu, Alhaji Muhammad S. Haliru Dantoro ( Kitoro IB) Mai Bargu ya tabbatar da sarautar Gado Da Masun Bargu ga Alhaji Suleiman Yahaya Babangida ( Cikasoron Minna).

A wata takardar da masarautar ta aikowa sabon Gado Da Masun, wadda mai martaba Kitoro ya sanyawa hannu, ta tabbatar da cewar kwazo da himmarsa da kokarin hada kawunan jama’a dan tabbatar da zaman lafiya tasa masarutar amincewa da nadin Suleiman Yahaya Babangida a matsayin Gado Da Masu.

Takardar ta cigaba da cewar a irin wannan lokaci da ake ciki ana bukatar mutane masu zuciyar taimakawa kasa da al’umma, dan haka masarautar Bargu tana alfahari da irinsu Suleiman Yahaya a matsayin ‘yan kasa na gari.

Tunda farko dai Alhaji Suleiman Yahaya Babangida, wanda shi ke rike da sarautar Garkuwan Talban Minna, ya samu karramawa daga masarautar minna da sarautar Cikasoro wanda ita ce irinta ta biyar a masarutun kasar Hausa, ranar 1 ga watan julin nan masarautar Bargu ta karrama shi da sarautar Gado Da Masu wanda ake sa ran nadinsa bayan sallah da kwana biyu.

Da yake bayani a fadarsa, sabon Gado Da Masun Bargu kuma Cikasoron minna, ya jawo hankalin matasa da su guji shiga harkokin da zai gurbata rayuwarsu, yace wani bala’in da ya shigo cikin al’umma a yau shine shaye-shaye wanda abin har ya shafi matan aure na cikin gida wanda wannan bakaramin fitina ba ne a cikin kasa.

Alhaji Suleiman Yahaya Babangida ya yabawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari akan kokarin farfado da tattalin arzikin kasar nan da ta sanya a gaba, yace akwai bukatar masu hannu da shuni da su taimakawa gwamnati wajen bude masana’antu dan baiwa jama’a ayyukan yi. Yace kowa na da rawar takawa ga cigaban kasa, har ma’aikacin gwamnati mai karamin albashi na da gudunmawar bayarwa komai kankantarsa, amma rashin tausayi da hangen nesa yasa kowa yana ganin sai ya wadatu sosai zai iya taimakawa marasa karfi wanda wannan babban kuskure ne.

Da ya juya kan sarautu kuwa, yace akwai bukatar duk wanda masarauta ta karrama ma shi da sarauta, yasan darajar sarautar nan da masarauta wajen hada kan jama’a samar da hanyoyin cigaban tattalin arzikin kasa da taimakon masarauta wajen ciyar da al’umma gaba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai