Dalilinmu Na Karbar Lambar Karramawa Daga Gwamnati – Iyalan Gani Fawehinmi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Dalilinmu Na Karbar Lambar Karramawa Daga Gwamnati – Iyalan Gani Fawehinmi

Published

on


Iyalan marigayi Gani Fawehinmi sun yi maraba da lambar karramawar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ba marigayyin.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya sanar da cewa, za a karrama marigayyi Mista Fawehinmi da lambar “Grand Commander of Nigeria (GCON)” a wani taron da za a gudanar ranar 12 ga watan Yuni na 2018 a Abuja.

Babban dan marigayin, Mista Mohammed, ya bayyana haka a sanarwar daya raba wa mane ma labarai, inda ya ce, iyakansu gaba daya sun amince sun kuma rungumi wannan karramawa ta GCON da aka yiwa mahaifinsu.

Fawehinmi, wani babban lauyan Nijeriya ne, ya kuma rasu a watan satumba ba 2009 bayan ya yi fama da cutar kansa ta huhu, yana kuma da shekara 71 Allah ya yi masa rasuwar.

Dangantakar Fawehinmi da wanda ya ci zaben 12 ga watan Yuni da kuma wannan karramawar da aka yi “muna a halin yanzu yasa ba zamu iya watsi da karramawar ba kamar yadda aka yi dana baya.

“Karbar wannan karramawar, wani cika buri ne ga zuriyyarmu”

“Wannan karramawar na zuwa ne daidai lokacin ake tabbatar wa Abiola cinye zaben 12 ga watan Yuni da aka gudanar shukarun baya”

“Da wannan lokacin ya zama na matukar farin ciki ga mahaifina, saboda abin da yake hankoron faruwarsa Allah ya tabbatar da shi” inji Fawehinmi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai