EFCC Ta Yi Wa Diezani Tonon Silili A Kotu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

EFCC Ta Yi Wa Diezani Tonon Silili A Kotu

Published

on


Hukumar EFCC ta shaida wa Babban Kotun Tarayya dake Abuja yadda ta bankado gidaje 19 wadanda ta yi zargin mallakin tsohuwar ministar albarkatun Man Fetur ne, wato Diezani Alison-Maduke.

Hukumar ta EFCC ta bayyana wa kotun cewa, wadannan gidajen guda 19 suna da matsuguni a kasashen Nijeriya, Amurka da kuma Ingila.

Cikin tonon sililin da Hukumar EFCC ta yi akwai batun cewa Babban Daraktan Bankin ‘First Bank’ , Mista Dauda Lawal ne ya taimakawa tsohuwar Ministar wurin siyan wadannan gidaje a Birnin Landan.

Haka kuma Hukumar ta EFCC ta kara da cewa, Kamfanin ‘Benedict Peters’ wanda ya kasance kamfanin kwangilar Kamfanin NNPC a zamanin da Diezani take a matsayin minista; ya ba tsohuwar ministar cin hancin dala miliyan 60 wanda aka hada wurin ba jami’an zabe cin hanci a kakar zaben shekarar 2015.

Gidajen da hukumar ta zargi Diezani da mallaka a Nijeriya, ta bayyana cewa matsuguninsu na Legas, Abuja da Fatakwal.

Hukumar ta kara da shaidawa kotu cewa ta iya kwato dala miliyan 400 daga hannun Benedict Peters, a binciken da take tsaka da gudanarwa kan badakalar.

Hukumar EFCC ta ce, Peters ne masu mallakin wasu kamfanoni biyu da aka yi musu rajista a kasashen waje; kamfanin ‘Collinwood limited’ da ‘Rosewood Inbestment Limited’ da kuma wani kamfanin Nijeriya mai suna ‘Aiteo Energy Resources’.

Hukumar EFCC ta koro wadannan bayanai ne a wata takardar da ta gabatarwa mai shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, domin ta janye hukuncin dakatar da kwace wasu gidaje mallakin Diezani  dake Amurka da Ingila.

Sai dai kamfanin Peters ya musanta wannan zargi na EFCC, inda ya bayyanawa kotun cewa wasu daga cikin gidajen ba na Diezani bane, mallakin kamfanin ne.

Advertisement
Click to comment

labarai