Falana Ya Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Sanya Hannu A Yarjejeniyar “Western Sahara” Da Kasar Maroko — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Falana Ya Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Sanya Hannu A Yarjejeniyar “Western Sahara” Da Kasar Maroko

Published

on


Babban lauyan Nijeriya, Femi Falana, ya gargadi gwamnatin tarayya da kada ta kuskura ta sa hannu a kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin wannnan gwamnatin dana kasar Maroko a kan ma’adanan da Allah Ya mallakawa yankin “Western Sahara”.

Falana ya kara da cewa, kotu zata iya yin fatali da yarjejeniyar a nan gaba.

A sanarwar da Mista Falana ya raba wa manema labarai jiya, ya ce, ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da ziyararsa zuwa kasar Maroko don matsa musu su tabbatar da ‘yancin cin gashin kan yankin “Saharawi Arab Democratic Republic”.

“Haka kuma, ya kamata a jawo hankalin shugabannin Nijeriya a kan hukuncin da kotun Turai na “European Court of Human Rights” da kuma babban kotun kasar Afrika ta kudu, wadanda suka yanke hukuncin cewa, kasar Maroko bata da hurumin tatsar ma’adamai dake dankare a yankin “Western Sahara” don ma’adanan mallakin mutanen yankin Saharawi ne gaba dayansu. Saboda haka kada gwamnatin tarayya ta shiga wani yarjejeniya da kasar Maroko a kan hakan ma’adanan dake yankin da kasar Maroko , saboda yarjejeniyar zai iya zama fanko da zaran an shiga kotu mai karfi” inji Falana.

Dan rajin kare bil’adam din ya kuma zargi gwamnatin tarayya da kaucewa matsayinta a kan yankin “Western Sahara”., ya lura da cewa, “A shekarar 1984, rusasshiyar gwamnatin sojoji karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari, ta goyi bayan kokarin mutanen yankin Western Sahara na nema wa kansu ‘yanci daga mulkin mallaka da ake yi musu, abin daya tabbatar da shigar da kungiyar “Saharawi Arab Democratic Republic” cikin kungiyar hadin kan Afrika ta “Organisation of African Unity (now African Union)”.

“Da suke kalubalantar shigab da kasar Saharawi Arab Democratic Republic cikin kungiyar OAU, kasar Maroko ta janye kanta daga kungiyar gaba daya. Wannan matsaya ta Nijeriya, ta samu ne saboda matsayan majalisar dinkin duniya da kuma hukuncin da babban kotun duniya ta yanke a shekarar 1975, inda ta yanke cewar, Western sahara bata cikin kasar Maroko, amma a wani kauce wa matsayar kasar nan a kan harkokin kasashen waje, gwamnatin Buhari bata kalubalanci bukatar kasar Maroko na neman sake dawo wa cikin kungiyar “African Union” ba.”

“Kasar Maroko na matsin lamba ga kasashen Afrika don su goya mata baya a kokarinta na ci gaba da mamaye yankin “Western Sahara”.  Haka kuma kasar ta Maroko na yawan kawo katsalandan a tarukkan kwamitocin majalisar “African Union” inda sukan bukaci a kori wakilan kasar “Saharawi Arab Democratic Republic” da nufin hana su halartar tarukan.

“In aka lura da shashi na 20 (1) na dokokin “African Charter on Human and People’s Rights” wanda ta samar da cewa, mutanen Afrika nada cikakken ‘yancin cin gashin kansu bay tare da wani tsamgwaba tare da ‘yan ci gaba da neman wa kansu ‘yanci a faninn tattalin arziki da siyasa, saboda haka, Nijeriya nada hakkin goyon bayan gwagwamaryar da mutanen yankin Western Sahara da karkashin mulkin mallakan kasar Maroko.”

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!