Faransa Da Jamus Za Su Magance Rikicin Ukrain — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Faransa Da Jamus Za Su Magance Rikicin Ukrain

Published

on


A kokarin dinke barakar da ake fama da ita a kasar Ukrain mai fama da ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha, kasashen Faransa da Jamus sun amince su hadu da bangarorin masu hamayya da juna domin lalubo bakin zaren magance matsalar. Ministocin harkokin wajen kasashen Ukraine da Rasha za su hadu da na kasashen Jamus da Faransa yau a birnin Berlin na kasar Jamus domin kokarin magance rikicin Ukraine wanda ya raba bangarorin biyu. Ya zuwa yanzu dai a kalla mutane 10,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin na Ukraine tsakanin masu goyan bayan Rasha da ke neman ballewa daga kasar da kuma dakarun gwamnatin.

Shugaba Bladimir Putin ranar alhamis ya yi gargadi kan duk wata takala daga Ukraine a dai-dai lokacin da kasar ke shirin fara daukar nauyin gasar cin kofin duniya da za’a fara a wannan makon. Fadan da aka yi ta tafkawa shekaru da dama da suka gabata a tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar Ukrain ne ya kai ga harbo jirgin Jigilar kasar Malesiya da har yanzu ba’a san ko wa za’a dora wa laifin ba. A kwanan nan dai an ambato wasu kasashen Turai na dora laifin ga kasar Rasha, a yayin da Rashar ke cewar su gabatar da hujja da shaidu mai karfi a maimakon magangannun fatar baki.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!