Fashola Ya Yi Alkawarin Gyara Gadar Da Ta Rushe Cikin Awanni 72 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Fashola Ya Yi Alkawarin Gyara Gadar Da Ta Rushe Cikin Awanni 72

Published

on


Ministan ayyuka, lantarki da gidaje, Raji Fashola, ya ce, nan da awanni 72 gadar da ta rushe a tsakanin Mokkwa zuwa Jebba, za ta koma daidai.

Fashola, ya shaida wa manema labarai hakan ne a Zariya, ta Jihar Kaduna, jim kadan da ya kai wa Sarkin Zazzau, Shehu Idris, ziyarar bangirma a fadarsa ranar Lahadi.

Kafin dai Ministan ya ziyarci Sarkin na Zazzau, sai da ya kaddamar da wani sabon inji raba hasken lantarki mai karfin, 60MBA/132/KB, wanda zai inganta samar da lantarkin a garin na Zariya.

Hukumar lura da kare aukuwan hadurra ta kasa ce ta sanar da masu motocin rugujewar gadar wacce ke bayan mahadar Mowo, da ke kan hanyar Mokkwa zuwa Jebba, a sakamakon ruwan sama ,mai yawa.

Fashola, ya alakanta rushewar gadar ne da canjin yanayi.

“Mun san hakan zai wahalar da matafiya a kan hanyar, muna ba su hakurin hakan, wannan lamari ne na gaggawa, muna kuma bin sa cikin gaggawan.

“Shekara guda da ta gabata, ranar 10 ga watan Yuni, gadar Tatabu ma ta rushe saboda ruwan sama mai tsanani, ita ma nan da nan muka gyara ta.

“Mun gyara ta, muka kuma sake gina wata babbar gadar da ta ma fita. Wannan ma hakan ne za mu yi mata.

“Daga bakin ‘yan kwangilarmu da kuma ma’aikatanmu, duk mun san abin da ya kamata mu yi, tun da na sami labarin aukuwar lamarin da safiyar nan, tuni har ma’aikatanmu sun isa wajen.

“Tuni mun umurci daraktanmu mai kula da shiyyar Arewa ta tsakiya, da ya hanzarta isa Jihar Kwara ya sadu da ‘yan kwangilar da ke Jihohin Neja da Kwara.

“Tabbas za a dan sha wahala kadan, amma dai za mu yi duk abin yi, ina da tabbacin komai zai koma daidai cikin ‘yan kwanaki kadan.

“Nan da awanni 72, ina da tabbacin za mu daidaita komai da za mu iya kulawa da wajen.

“Daraktan namu na shiyya zai rika sanar da mu halin da ake ciki a dukkanin awanni 12, don haka babu wani abin firgici a cikin lamarin.

“Lamari ne da ya faru saboda ruwan sama mai yawa. Ruwan sama ya yi mana barna, amma kuma ai masuntanmu su hakan alheri ne a gare su,” in ji Fashola.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!