Gwamnatin Tarayya Za Ta Sallami Baragurbin Malamai A 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sallami Baragurbin Malamai A 2019

Published

on


Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya bukaci malaman makarantu da su tabbatar da cancantar su, takardunsu da kuma rajistarsu kafin nan da shekarar 2019, ko kuma a kore su daga ajujuwa.

Adamu Adamu, ya yi wannan gargadin ne lokacin da yake duba kashi na farko na wannan shekarar na jarabawar cancantar malaman, a Abuja, ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kawo rahoton cewa, akalla malaman da ake nufin dauka dubu 22,000, ne za su dauki jarabawar wacce za a yi ta da na’urar kwamfuta ranar 7 ga watan Yuni zuwa 9 ga watan.

Ministan wanda Sakataren ma’aikatar na shi, Sonny Echono,  ya wakilce shi, ya karfafa cewa, matukar malamai ba su cancanta ba, to ba ta yadda za a yi dalibai su sami wani ilimi nagari, kasar kuma ita ne za ta cutu.

“Hakan ne ya sanya a gwamnatance muke dagewa da daukaka darajar lamarin, tilas ne mu zama tamkar sauran kasashen duniya.

“Duk malamin da bai tabbatar da cancantarsa daga nan zuwa shekarar 2019 ba, za mu fitar da shi daga aji ne kawai. Mu saka wadanda suka cancanta.

“Abin kunya ne a garemu, muna da mutanan da suka cancanta masu yawa, amma duk ba su da aikin yi, ga kuma aikin amma a hannun wadanda kuma ba su cancanta ba.

“A baya, ba mu da wadanda suka cancantar isassu, shi ne muke cike gurbi da baragurbin su domin su cike gurbi kawai, sararin da suka samu kenan kawai.

Ministan ya ce, wasu mutane suna ta sukan yi wa malaman jarabawa da kwamfuta, wanda ya ce, ba kuma za a fasa hakan ba.

A cewar shi, duk duniya, hatta a daliban makarantun Firamare, suna amfani ne da kwamfutan da makamantan ta.

Ministan ya ce, duniya fa ba za ta tsaya jiran Nijeriya ne ba, don haka ya nemi kowa a makarantun namu da ya yi kokarin daukaka matsayinsa.

“Muna fama da matsalan tulin malaman da suke jiran daukar jarabawar, wanda hakan ma yana da kyau.

In akwai bukata za mu yi abin har kashi na uku, don dai mu tafi da kowa.

Magatakardan hukumar rajistan malamai ta kasa, Josiah Ajiboye, , ya ce za a gudanar da jarabawar ne a cibiyoyi 42 da Jihohin kasarnan 36 har da birnin tarayya bi-da-bi.

Josiah Ajiboye, ya ce wasu Jihohin ma sun fara gudanar da jarabawar a ranar 7 ga watan Yuni, kasantuwar yawan masu daukar jarabawar su,

Ya lissafa Jihohin da suka fara din kamar haka, Bauci, Enugu, Kaduna, Kano da Taraba.

“A Jihar Kaduna, muna da masu daukar jarabawar 6,000, a Jihar Kano, muna da kimanin 2,000, Jihar Enugu, muna da 3,600, Taraba kuma muna da 2,000.

“Za a yi jarabawar ne cikin mintuna 60, a amsa tambayoyi 60.

“Muna kuma da bayanan duk abin da ke gudana a Jihohin, kuma komai na tafiya lami kalau.

Ajiboye, ya ce an shirya jarabawar ce daidai da ilimin masu daukar jarabawar, da suka hada da masu, NCE, Digiri, Digiri na biyu, da kuma masu ilimin karatun Farfesa.

Da yawan wadanda suka rubuta jarabawar da suka yi magana da wakilinmu, sun nuna jin dadinsu da yadda jarabawar ta gudana.

Sai dai, kadan daga cikinsu suna da matsalan yin amfani da Kwamfuta, wanda hakan ya sanya suka kasa kammala jarabawar na su kafin cikan lokaci.

Akalla mutane 900 ne suka rubuta jarabawar a babban birnin tarayya Abuja.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!