Harin Makami Mai Linzami Ya Hallaka Fararen Hula A Saudiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Harin Makami Mai Linzami Ya Hallaka Fararen Hula A Saudiya

Published

on


Hukumomin kasar Saudiya sun ce fararen hula uku sun hallaka a garin Jizan da ke kudancin kasar, a wani harin makamai mai linzami da ake kyautata zaton cewa ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen ne suka kai. Kakakin rundunar sojin Saudiya, Kanal Turki al-Maliki ya ce da gangan mayakan na Houthi suka kai harin kan fararen hular a daren jiya Asabar.

A ‘yan watannin baya-bayan nan dai, mayakan na Houthi sun harba makamai masu linzami cikin Saudiya a lokuta daban-daban, in da wasu suka fada babban birnin kasar Riyadh. A watan Maris na shekarar 2015, Saudiya ta kaddamar da yaki kan ‘yan tawayen na Houthi, bayan da suka hambarar da gwamnatin waccan lokaci da ke birnin Sana’a. Yakin da bangarorin biyu ke ci gaba da gwabzawa ya haddasa hasarar sama da rayukan fararen hula 10,000 a kasar Yemen, yayin da kuma ya haddasa bala’in yunwa da barkewar cututtuka a yankunan kasar, wanda yin hakan ya biyo bayan rufe kan iyakokin Yemen din da kowane bangare ya yi, in da yake da karfin iko.

 

Advertisement
Click to comment

labarai