Messi Zai Yi Ritaya Idan Har Argentina Ba Ta Yi Kokari Ba A Kofin Duniya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Messi Zai Yi Ritaya Idan Har Argentina Ba Ta Yi Kokari Ba A Kofin Duniya

Published

on


Dan wasan gaba na kasar Argentina, Leonel Messi, ya bayyana cewa cigaba da bugawa kasar sa ta Argentina wasa ya danganta da yadda sukayi kokari a gasar cin kofin duniya da za’a fara a sati mai zuwa

Messi, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyar a tarihi yayi ritaya a baya, bayan da kasarsa tayi rashin nasara a wasan karshe na cin kofin nahiyar kudancin Amurka karo na biyu a jere a hannun kasar Chile sai dai daga baya ya janye kuma ya ci gaba da wakiltar kasar.

Argentina dai tasha kashi a hannun kasar Jamus a wasan karshe na cin kofin na duniya shekaru hudu da suka gabata wanda hakan yasa ake ganin abune mai wahala su sake samun damar zuwa wasan na karshe a wannan karon.

Sai dai Messi ya ce bazaice komai ba a game da ritayarsa sai abinda suka buga a gasar ta bana idan sunyi kokarin da duniya zata amince dashi zai cigaba da bugawa kasar wasa idan kuma aka samu akasin haka kawai zai hakura.

Yaci gaba da cewa kafafen yada labaran kasar ne basa yi musu adalci wajen kawo rahoto amma sunje wasan karshe na cin kofin nahiyar kudancin Amurka sau biyu sannan sunje na gasar cin kofin duniya amma ba’a yabawa yan wasan.

Yace kowa yasan burinsu shine na lashe gasar amma kuma duk wanda yaje wasan karshe ai yakamata a yaba masa da irin kokarin da yayi har yaje wasan na karshe inda yace wasan karshe ba karamin abu bane.

A kwanakin baya shugaban kasar ta Argentina, Mauricio Sacri ya bayyana cewa  ne kawai da Messi zai iya tabbatar musu cewa ko zasu iya lashe gasar sai dai Messi ya ce watakila wannan ne kofin duniya na karshe da zai bugawa kasarsa.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!