NAPTIP Ta Yi Babban Kamu, Ciki Har Da Dan Sanda — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

NAPTIP Ta Yi Babban Kamu, Ciki Har Da Dan Sanda

Published

on


Jami’an hukumar hana fataucin mutane ta kasa, (NAPTIP), sun yi nasara dakile wasu mutane 10 da ake kokarin haurewa da su Mosko, ta kasar Rasha, hukumar ne ta fadi hakan cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi.

Ranar Lahadi ne da dare aka gano su a tashar Jiragen sama ta Murtala Muhammad, cikin wani shiri da hukumar ke gudanarwa mai suna, ‘Operation BLOCK’ lokacin da ake kokarin shigar da mutanan wani Jirgin saman kasar Turkiyya, zuwa kasar ta Rasha, inda aka fake da zuwa kallon wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya.

Mutanan da aka ceto din sun hada da wani matashin saurayi da kuma ‘yan mata tara.

Biyar daga cikinsu daga Jihar Edo ne suka fito, uku kuma daga Jihar Delta, sauran kuma daga Jihohin Imo da Binuwe.

Takwas daga cikinsu duk suna zaune ne a garin Benin, sauran biyun kuma suna zaune ne a garin Warri da Osogbo.

Hukumar ta ce, biyar daga cikinsu, da suka hada da, Esan Matthew, wani sajent na ‘yan sanda, da, Stephen Fayemiwo, wanda shi ma dan sandan ne, duk an kama su ne da laifin shirya tafiyar mutanan waje.

Uku kuma da suka hada da, Azeez Olowo, Idowu Fashakin da Eni Godwin, an kama su ne bisa laifin taimaka ma su.

A makon da ya gabata ne, babban daraktan hukumar ta NAPTIP, Julie Okah-Donli, ta ankarar da cewa, kungiyoyin masu mugun nufi suna amfani da sassaucin da aka yi na shiga kasar ta Rasha, domin wasannin kwallon kafan na duniya, wajen aikewa da matasan kasannan aikin bauta a kasar ta Rasha.

Ta kuma ce, jami’an hukumar sun dukufa ta yin amfani da rahotannin sirrin da suke samu wajen ganin sun dakile ayyukan kungiyoyin.

“Masu fataucin mutanan sukan matsa wa wasu matasa da iyayensu, su biya su wasu makudan kudade domin su nema masu bizar shiga kasar ta Rasha,” in ji Julie Okah-Donli.

Hukumar ta ce, ta jima tana bibiyar tattaunawar da ke gudana a tsakanin wadanda ake son fitarwar da kuma masu fataucin nasu, har sai da suka iso gurbin karshe na barin kasa ne a tashar ta Jiragen sama.

“An kawo hudu daga cikinsu ne Obalende, Lagos, a lokuta daban-daban ranar Juma’a daga Benin, ta Jihar Edo, a wani waje da ake kira kasuwar Sura, inda aka ajiye su a wani daki da ke anguwar ta Sura.

“Har ya zuwa ranar Asabar jami’an namu suna kan kula da su ba tare da sun sani ba, da misalin karfe 3 na yammacin ranar ne aka kwashe su zuwa filin saukar Jiragen saman.

Da isansu filin Jirgin saman ne da misalin karfe 5:25 na yamma, aka sauke su da kayansu tare da ‘yan rakiyar nasu biyu duk akan idon jami’an namu.

A nan ne, Messrs Fashakin da Olowo, suka fara kiraye-kirayen waya, sa’ailin da su kuma mutanan da za a yi fataucin nasu suke tsaye a wata kwana da ke wajen dakin hutawan matafiya waje har na kusan awa guda da rabi suna jiran umurni.

Jim kadan, sai Mista Olowo, ya sadu da wani mai suna, Eni Godwin, inda suka tattauna.

“Daga nan, sai wani mai suna, Mathew Esan, wanda muka gano jami’in ‘yan sanda ne ya sadu da Eni Godwin, da tsaye a gefe guda suka dan tattauna. Daganan sai, Mathew Esan, ya tafi wajen ‘yan matan ya tattauna da su, yana masu jawabi tamkar jawabin malami da dalibansa.

“Ba da jimawa ba ne da hakan, wani mai suna, Stephen Fayemiwo, wanda shi ma daga bisani muka gano jami’i ne na ‘yan sanda, ya zo wajen ‘yan matan ya yi masu magana ya kuma danka wa kowace daya daga cikinsu takardun tafiyar nasu, da suka hada da Fasfo, katin shaidar halartar wasannin kwallon kafar na Rasha da kuma tikitin Jirgin na Turkiya.

“Daga nan ne, ya jagorance su cikin dakin na matafiya ya kuma soma kokarin gabatar da dukkanin  bincike don shigar da su Jirgin saman na Turkiya, inda a nan ne aka fara kama shi.

“An kama shi tare da dukkanin wadanda suke shirin fitarwar da kuma sauran abokanin burmin na shi wadanda suke kan kulawar jami’an namu.

“Dukkanin su an kai su ofishin jami’an tsaron tashar Jiragen saman inda aka dauki bayanan su kafin a mayar da su ofishin hukumar ta NAPTIP da ke Legas, domin ci gaba da gudanar da bincike. Jami’an hukumomin tsaro na, tashar Jiragen saman, DSS, JBTE, duk sun taimaka wajen bin diddigi da kuma kamun na su.

Advertisement
Click to comment

labarai