Sabon Harajin Giya Da Sigari Ba Yana Nufin Takura Masu Masa’anantun Cikin Gida Ba Ne – Gwamnatin Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sabon Harajin Giya Da Sigari Ba Yana Nufin Takura Masu Masa’anantun Cikin Gida Ba Ne – Gwamnatin Nijeriya

Published

on


Ma’aikatan kudi ta Nijeriya ta ce, karin da aka yi wa harajin giya da sigari ba ana nufin takurawa masu masa’anantun cikin gida bane, LEADERSHIP A Yau ta gano cewa, sabon tsarin harajin zai rafa aiki ne daga yau Litinin.

Ministan Kudin, Kemi Adeosun, ta ce, an shirya sabon tsarin harajin zai aiki ne na tsawon shekarar 3, daga 2018 zuwa 2020 saboda a sami sanya ido a kan yadda tsarin yake tafiya wajen tsakaita kudaden kayayyakin.

Ta kuma kara da cewa, a karkashin wannan tsarin bayan karin kashi 20 na kudin tallace talace, kowanne karan sigari zai fuskanci harajin naira 10, abin nufi anan shi ne kwalin sigari mai kara 20 zai fuskanci naira 20 a matsayin haraji a shekarar 2018.

A shekarar 2019, za a caji naira 2 a kan karan sigari ko kuma naira 58 a kan kwali mai kara 20. Ministan ta kuma kara bayyana cewa, a shekarar 2020 kowanne karan sigari zai fuskanci harajin  naira 2.90 abin dake nuna cewa, kwalin sigari mai kara 20 zai fuskanci harajin naira 58.

Sanarwar dama’akatan kudi ta fitar ranar Lahadi, ta yi bayanin cewa, barasa da sigarin da aka shigo dasu daga kasashen wajen zasu fi fuskantar haraji mafi tsoka.

“Koma bayan bayanan da wasu keyi na cewa, an shirya kudadaen harajin ne don gallawa masu masa’antun kasashen waje, an dankarawa kayyayakin barasa dana sigarin da ake shigo wa dashi daga kasashen waje kashi 60 na kudin haraji, wadannan mataki ne da gwamnati ta dauka don karfafa masu masa’nantun cikin gida” inji jam’in watsa labaran ma’aikatan, Hassan Dodo.

 

Advertisement
Click to comment

labarai