Sojoji Sun Tarwatsa Garken Barayin Shanu A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Tarwatsa Garken Barayin Shanu A Kaduna

Published

on


Rundunar sojojin Nijeriya ta ce, dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da kwato mashinnan hawa 36 daga ‘yan ta’addan a karshen makon daya gabata, a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Dakarn sun rutsa da ‘yan ta’adda ne a yayin da suka shiga garin Dogon dawa ranar kasuwar garin don satan abinci.

Jami’in watsa labaran rundunar sojojin Nijeriya, Birgedia Janar Tedas Chukwu, ya sanar da haka inda ya kara da cewa, an kuma kwato wayar tafi da gidanka guda 5 da kudi Naira 9,135 daga hannun ‘yan ta’addan.

A yayin gudanar da kanmu na ‘Idon Raini’ inda muke binciken masu zirga zirga, dakarun runduna ta “1 Dibision Garrison Kaduna” sun cafke wani mai suna Abdulkadir Samaila na garin Dogon Dawa wanda ke aikin samar wad a ‘yan ta’addan kayayyaki aiki, sun kuma kama wani suna Alhaji Yahaya, wanda ke samar wa da ‘yan ta’addan mayan aiki.

Cikin abubuwan da aka kama  a hannun ‘yan ta’addan sun hada da wayar hannu guda 2 da mota kirar ýone Opel da kuma kudi naira N34,000.

A farmakin da aka kai kauyen Sabon dakarnmu sun kashe ‘yan ta’adda 3, dakarun namu sun kuma kwace wayoyin hannu 4 da wasu na’ura mai kama da ruwan “Gam” suka kuma kashe mutum 3.

Chukwu ya kuma tabbatar da kudurin sojojin Nijeriya na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa a kowanne lokaci.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!