Zancen Banza Ne Cewa APC Yobe Ta Kasu Gida Biyu –BOGON — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Zancen Banza Ne Cewa APC Yobe Ta Kasu Gida Biyu –BOGON

Published

on


Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Bursari, Gaidam da Yunusari a majalisar wakilai ta kasa- a jihar Yobe, Goni Bukar Lawan, ya karyata wani rahoton da wata kafar yada labarai, a shafukan sada zumunta, wanda a ciki ta ce yan majalisar tarayya daga jihar sun nuna rashin gamsuwar su da zaben sabbin shugabanin APC da ya gudana.

A cikin wata takardar bayani wadda dan majalisar wakilan ya rattaba wa hannu, a ranar Lahadi (jiya), ya bayyana cewa dole ya fito fili ya karyata wancan ikirari domin jama’ar da ke wajen jihar Yobe, domin gudun kada wannan labarin ya  shammace su- wannan rahoto zuki ta malle ne.

“abu na farko dangane da wannan lamari shi ne, sananne abu ne ga duk mai bibiyar siyasar jihar Yobe, kan cewa na kasance mutum mai biyayya dari bisa dari zuwa ga jagoran mu, Gamma Ibrahim Gaidam”.

Ya ce, bugu da kari Kuma, sanin kowa ne kan cewa biye yake sau da kafa, a dukkan zabukan da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar Yobe; a matakin unguwanni, kananan hukumomi da jiha, da daukwacin masu ruwa da tsaki a sha’anin jam’iyyar, da ya hada har da ni kaina, wanda zabuka ne da suka gudana cikin gaskiya da yanci ga kowa.

“a kowanne lokaci burin Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam, shi ne jam’iyyar APC ta kasance dunkulalliya da kyakkyawan tsarin shugabanci mai cike da mutane masu dattaku.Saboda haka, ni a guna, bai kamata wannan rahoton rashin kan gado; cewa wai jam’iyyar APC a Yobe ta rabu gida biyu ya rudi jama’a ba, su yi watsi dashi.”

“idan har wannan zancen cewa APC a Yobe ta rabu gida biyu, me zai hana a ga alamun hakan a zahiri. A sha’anin siyasa, duk lokacin da aka ce akwai bangarori dole kowa ya ga hakan a fili, saboda ba a taba samun rarrabuwar kai baki alaikum ba. Haka zalika kuma, babu wani sabani a tsakanin yan APC, kuma a can baya irin wannan bai afku ba- dunkule muke tun a tsohuwar ANPP.” Inji shi.

“mu a nan jihar Yobe, muna yin al’amuran mu ne ta hanyar hadin kai, kuma a matsayin yan gida guda. Kuma duk yadda lamurra suka yi zafi, a karshe zai bar mu tare, masu magana da murya daya- ba tare da sabani ba”.

“kuma Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam shi ne jagoran wannan tafiya kuma mun yarda dashi dari bisa dari tare da salon sa na shugabancin wannan dunkulallen gida, jihar Yobe. Amma muna hasashen wasu da hakar su ta kasa cimma ruwa a jam’iyyar APC, sune ke kokarin haddasa rikicin cikin gida, wanda kuma sun daba a kas- ba zasu yi nasara ba. Saboda haka, gani nan bari nan; farar tumfafiya”. Inji Goni.

Wanda a karshe, dan majalisar ya bukaci magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Yobe da cewa su ci gaba da baiwa Gwamna Gaidam cikakken goyon baya a ayyukan sa na bunkasa jihar Yobe.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!