An Kafa Tarihi: Trump Da Kim Jong Un Sun Hadu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

An Kafa Tarihi: Trump Da Kim Jong Un Sun Hadu

Published

on


A karon farko kuma a wani mataki na kafa tarihi, shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un sun hadu.

Shugabannin biyu sun hadu ne da safiyar ranar Talata (lokacin Singapore), inda suka gaisa a gaban totocin kasashen biyu da aka jera a bayansu.

Daga baya kuma sun shiga cikin otel din da taron ke gudana, inda suka fara tattaunawa kan batun da ake tsammanin na kwance damarar makaman nukiliyan Korea ta Arewa ne.

Amma gabanin hakan, shugaba Trump da Kim, sun dan zauna na wani lokaci domin ganawa da manema labarai.

“Lallai ba abu mai sauki ba ne zuwa nan.” Inji Shugaba Kim.

Ya kara da cewa, “zamanin da ya shude ya haifar mana da kalubale kan yadda za a samar da maslaha, amma kuma mun yi hobbasa mun tsallake duk wani shinge, yanzu kuma ga mu a nan yau.”

Shi kuwa shugaban Amurka ya jaddada abin da Kim ya fada ne yana mai cewa, “wannan gaskiya ne.”

Trump ya kara da cewa, “lallai za mu cimma gagarumar nasara, kuma wannan abin alfahari ne, kuma ba na wata tantama, za mu kulla kyakkyawar dangantaka.”

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a daren ranar Talata shugaba Trump zai bar kasar ta Singapore.

Advertisement
Click to comment

labarai