Fellaini Ya Yanke Shawarar Barin Manchester United — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Fellaini Ya Yanke Shawarar Barin Manchester United

Published

on


Rahotanne daga kasar Belgium sun bayyana cewa Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Maroune Fellaini, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin kungiyar a karshen kaka mai kamawa bayan da kwantaraginsa zai kare a akungiyar a cikin watan Yulin wannan shekarar.

Fellaini, mai shekara 30 yakoma Manchester United ne daga kungiyar kwallon kafa ta Eberton a shekarar 2013 shekarar da tsohon mai koyar da kungiyar Dabid Moyes, ya karbi aikin kungiyar ta United bayan ritayar Sir Aled Ferguson.

A wannan kakar Fellaini yasha fama da ciwo inda a yanzu yake kasar Rasha domin wakiltar kasarsa ta Belgium a gasar cin kofin duniya wanda za’a fara a ranar Juma’a.

Mai koyar da’ yan wasan kungiyar, Jose Mourinho, ya bayyana cewa dan wasan yanada amfani a kungiyar wanda hakan yasa kuma bazasu yarda su rabu da dan wasan ba.

Sai dai dan wasan ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar sakamakon rashin buga wasanni akai-akai a kungiyar inda tuni ya yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Basiktas dake kasar Turkiyya domin cigaba da buga wasaninsa a kungiyar.

Tuni dai kungiyar ta amince da siyan dan wasan Shakhtar, Fred domin maye gurbin na Fellani yayinda kuma har ila yau take zawarcin dan wasan tsakiya domin maye gurbin Macahel Carrick wanda ya yi ritaya a karshen kaka.

Advertisement
Click to comment

labarai