Garba Lawal Yaba Wa ’Yan Wasan Nijeriya Shawara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Garba Lawal Yaba Wa ’Yan Wasan Nijeriya Shawara

Published

on


Yayin da ake tunkarar gasar cin kofin duniya  da za’a fara a kasar Rasha nan da kwana biyu, tshon dan wasan tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Garba Lawal, ya yi tsokaci game da yadda ya kamata ‘yan wasan Nijeriyar na yanzu su tunkari gasar.

A wata hirar da ya yi da manema labarai, Lawal, wanda yake cikin wadanda suka wakilci Nijeriya a gasar a shekarar 1998, ya nuna cewa kada ‘yan wasa su damu da tsoron jin ciwo in suna son taka rawar gani sosai.

Lawal ya ce dabarar wasa a hankali a cikin fili ba zai taimaki dan wasa ba wajen kaucewa rauni domin tsautsayi na iya zuwa ko ta wace hanya.

Tsohon dan wasan Roda JC na kasar Holland din ya ce duk wanda yaje gasar na son ya ci gasar saboda haka kowa zaiyi iya yinsa wajen ganin kasarsa tazama zakara a gasar.

Sai dai kuma dan wasan ya ce ko wane dan wasa ya san lokacin da ya kamata ya huta bayan ya dawo daga atisaye domin samun isasshiyar lafiya da hutun da jikinsa ke bukata.

Sannan kuma ya ce dole sai yan wasan sun saka zuciya da kishin kasa idan har sunason samun nasara domin miliyoyin yan Nijeriya suke wakilta kuma duk abinda yafaru na farin ciki sune haka duk abinda yafaru na rashin jin dadin gasar laifinsu za’a gani.

Advertisement
Click to comment

labarai