Hukumar  Magunguna Ta Kaduna Da Jami’ar KASU Za Su Kafa Cibiyar Horas Da Dalibai Akan Tsarin Rabar Da Magunguna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Hukumar  Magunguna Ta Kaduna Da Jami’ar KASU Za Su Kafa Cibiyar Horas Da Dalibai Akan Tsarin Rabar Da Magunguna

Published

on


Hukumar kula da magunguna da rabar da kayan kiwon lafiya mallakar gwamnatin jihar Kaduna da jami’ar jihar Kaduna KASU suna shirin kafa cibiya a harabar hukumar da zata dinga horas da dalibai akan tsarin rabar da magunguna a jihar.

Babbar  Sakatariyar Hukumar Ramatu Abdulkadir ce ta shedawa manema labarai hakan a lokacin da ta kai ziyara ta musamman a jami’ar KASU.

Ramatu ta yi nuni da cewar idan aka kafa cibiyar horasawar, zata baiwa daliban da za a dauka damar sanin makamar aiki na rabar da magunguna wanda ya yi dai dai dana fadin duniya.

A cewar ta, cibiyar da za a kafa nan gaba, zata kuma zamo wajen koyar da daurssa da kwararru na gajeren zango akan rabar da magunguna.

Ramatu ta sanar da cewar tuni gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da tsarin rabar da magunguna ga asibitocin gwamnati, musamman don a tabbatar wadanda sun kai ga wanada ya kamata su amfana a cikin sauki tare da kuma kawar da yin asara.

Ta kuma sanar da cewar sakamakon tsarin na rabar da magunguna, hakan ya taimaka wajen rage yawan ranakun da ake batawa wajen rabar da magungunan zuwa ga cibiyoyin kiwon lafiya guda hamsin da shida daga kwana talatin da uku.

A karshe Ramatu ta jinjina wa gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Nasir El-rufai a kan goyon bayan da yake bai wa kwamitin aikin rabar da magunguna na jihar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai