Jam’iyyar PDM Ta Shirya Tsaf Don Fuskantar Zaben 2019 -Alhaji Mairiga Ango — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Jam’iyyar PDM Ta Shirya Tsaf Don Fuskantar Zaben 2019 -Alhaji Mairiga Ango

Published

on


Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDM a jihar Kaduna Alhaji Mariga Ango, ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta PDM ta kammala dukkan shirye- shirye don fuskantar zaben 2019, kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta fitar da jadawali kwanakin baya, Alhaji Ango, ya yi wannan tsokacin ne a yayin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a babban ofishin yakin neman zabensa dake garin Zariya.

Alhaji Mairiga Ango ya kara da  jawo hankalin al’ummar jihar Kaduna dasu tabbatar da sun mallaki katin zabe, su kuma tabbatar da sun zabi jam’iyyar PDM a dukkan matakan gwamnati. “Ya kamata kowa ya yi karatun ta natsu a kuma sa hankali wajen zaben ‘yan takarar da suka cancanta, wadanda za su gudanar da mulki cikin adalci tare da mutumunta addininmu da al’adunmu” inji shi.

Daga nan ya mika godiyarsa ga dimbin masoya  masu goyon bayansa a fadin jihar Kaduna, musamman matasa  maza da mata, ya yi alkawarin kirkiro da tsare-tsaren da za su bunkasa rayuwar al’umma idan Allah ya tabbatar masa da zama gwamnan jihar Kaduna a zaben dake tafe, “ Zamu samar da aiyyukan yi ga dimbin matasanmu tare da samar da ababen more rayuwa a dukkan fadin jihar inshaAllah, ina kuma kira ga al’ummar jihar Kaduna dasu gudanar da harkokin siyasa cikin natsuwa tare da mutunta ra’ayoyin juna, ta haka ne kawai zamu samu nasara, har mu ci moriyar dake tattatare da mulkin dimokradiyya” inji shi.

Game da kammala azumin watan Ramadan da shirye shiryen bukukuwan sallah kuma, Alhaji Ango, ya mika sakon fatan alhairi ga daukacin al’ummar Musulmin jihar Kaduna dama Nijeriya baki daya,  a bisa kawo karshen watan azumin Ramadan lafiya, ya yi fatan za a yi bukukuwan sallah cikin nasara, “Ina yi wa mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris tare da dukkan hakimansa fatan za a yi hawan sallah lafiya, Allah ya sada mu da dukkan alhairan dake cikin watan Ramadan”, daga nan ya kuma jawo hankalin jama’a musamma matasa dasu gudanar da bukuwan sallah lafiya su kuma guji tashe tashen hankali.

Advertisement
Click to comment

labarai