Ko Nijeriya Za Ta Sauya A Shekarar Nan? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

DAGA NA GABA

Ko Nijeriya Za Ta Sauya A Shekarar Nan?

Published

on


Hausawa na cewa “ Kowar tuna bara to bai ji dadin bana ba” sai dai wani lokacin ana tuna baran domin a kiyayi yadda banar zata kasance. Wannan filin zai yi bita ne kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a shekarar da ta shude domin a kiyayi faruwarsu a wannan shekarar, ko kuma su kasance komar tarihi da za su zama tsani na amfanuwar wannan al’ummar a gaba.

A shekarar da ta gabata ne Sojojin Nijeriya suka yi ikirarin kakkabe Boko Haram, tabbas a shekarar an ci karfin tsagerun Boko Haram, sai dai ikirarin kakkabe sun da aka yi shi ne abun da ba za a iya amincewa da shi ba, domin bayan yin ikirarin sai aka ci gaba da samun tayar da bamabamai da kunar bakin wake da garkuwa da mutane da su tsagerun Boko Haram din suka ci gaba da yi.

Abin dubawa a nan, ya kamata hukumomin kasar nan su rika tauna magana kafin furtata musamman ma kan abinda ya shafi tsaro, domin ita harkar tsaro ba harka ce da za a rika sa siyasa kanta ba, harka ce da ke bukatar sirri da jajircewa wajen tabbatar da gaskiyar abinda ke faruwa ga al’umma, an ce an kakkabe Boko Haram, mutane za su saki jikinsu su ci gaba da mu’amullar su to kuma sai ga wasu abubuwa sun ci gaba da faruwa, wadanda ke nuna rashin ingancin waccen maganar da aka yi da faro. Saboda haka ya na da kyau a wannan shekarar hukumar Sojojin Nijeriya kara himma bisa wadda su ke, na ganin cewa an kakkabe Boko Haram din ba farfaganda ba.

A shekarar da ta gabata ne Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a kasar nan, wanda wannan kuma alama ce da ta nuna cewa akwai matsalar tsaro a kasar nan, domin ba abun da ke kawo garkuwa da mutane sai rashin tsaro, tabbas a shekarar masu garkuwa da mutane sun ci karensu ba babbaka, sai da ta kai har DPO da wasu manyan jami’an gwamnati an yi garkuwa da su, wadanda suka hada da ‘yan majalissu da sauran makamantansu, kai wani abun bakin ciki har malamin makarantar Allo da almajiransa sai da a ka yi garkuwa da su a cikin shekarar da ta shude din. Tabbas 2017 shekara ce da ‘yan Nijeriya ba za su yi fatan abun da ya faru cikinta ta fuskar garguwa da mutane ya kara faruwa ba har a shafe tarihin Duniya.

Duk da cewa, daga baya, bayan da aka fara taba jami’an gwamnati an ta shi tsaye an fara yaki da abun inda har aka rika kama gungun masu wannan sana’a da kuma wani fitaccen mai garkuwa da mutane a Legos, amma dai a zahirin gaskiya sakakin gwamnati ne wajen rashin tsaro da inganta bangaren tsaron, duk da cewa mun san wannan kasa ba ta da wadatattun jami’an tsaron da za su iya ba da tsaro a duk inda ake bukata.

Wannan fili na fatan wannan shekara ta 2018 gwamnati ta bullo da wani shiri da zai taimaka wajen karuwar jami’an tsaro na ko wane irin fanni domin a samu ingantattar rayuwar walwala a wannan kasa tamu mai albarka. Babu shakka muna bukatar karin jami’an tsaro sosai a wannan kasa ta mu, kuma muna fatan muga karinsu a shekara nan da muke ciki, sannan wannan fili na kira ga Gwamnatin kasar nan da ta gyara tsarin albashin jami’an tsaron kasar nan ta yadda za si iya kawar da kansu daga amsar na goro, wanda shi ma zai taimaka matuka wajen bunkasuwar tsaro a wannan kasa, duk dai a kan wannan fanni na garkuwa da mutane ya kamata gwamnati ta samar da wani shiri da zai magance zaman banza ga wadanda ke zaune karkara ba su yi ilimin boko ba, A sama ma su wasu ayyuka da za su taimaka ma su wajen ganin sun dogara da kansu, wanda hakan zai taimaka wajen rage shigar su ayyukan ta’addanci.

Cikin munanan abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabace mu ba zai yiwu a wuce ba ambaci matsanaciyar tsadar kayan masarufi ba, wanda ake ta’allaka abun da tsadar Dala Eur, babu shakka al’ummar wannan kasa Allah ne ya cecesu kawai amma sun sha tasku a bangaren tsadar kayan abinci da sauran kayan masarufi, abubu suka linka kudi abinci ya karanta talauci ya samu mazauni a wannan kasa wanda hatta rowan sha na leda said a ya kara kudi, said a takai masu cin abinci sau uku a rana sun dawo biyu, masu ci so biyu sun dawo daya. Wannan tsadar rayuwa ita ta kara taimakawa wajen bullar ayyukan ta’addanci a wannan kasa tamu. Tabbas wanna rayuwa da aka samu kai a ciki ta sami asali ne ta dalilin rufe bodojin shigo da abinci da wannan gwamnatin ta yi domin a samu  a rage yawan amfani da kayan waje a wannan kasa. Amma matsalar sai kuma gwamnatin taki tanadar wasu kayan masarufin wanda zai ragewa mutane radadin da za su ji kafin a fara amfani da na gidan, dan haka wannan fili na bayar da shawara ga wannan gwamnati da ta tanadi hanyoyin magance faruwar urin wannan matsalar a wannan shrekara da muka shiga domin dadadawa al’ummar wannan kasa da suka sha iska da sanyi wajen zabenta.

A shekarar 2017 ne hukumar EFCC ta bullo da wani shiri na busa Usir ga barayin gwamnati, inda aka bada dammar cewa, duk wanda ya san wani ya saci kudin gwamnati kuma ya boye su a wani wuri to ya busa usir za a bashi wasu kaso daga cikin kudin, tabbas wannan shiri ya taimaka sosai wajen samun kudade daga wadanda suka saci kudaden gwamnati sosai, kuma ya taimakawa hukumar ta tara kudade, musamman wadanda aka samu a Ikoyi da na Kaduna da sauransu da dama, sannan hukumar ta yi tsari mai kyau dan gujewa wadanda ka iya yiwa wasu kazafi ko sheri. Sai dai fatanmu a wannan shekarar wannan aiki ya dore kuma a rika ba da kason wanda ya hura usir din kan lokaci, wanda hakan zai karawa mutane kwarin guiwa wajen fallasa irin wadannan mutane a duk inda suke.

A shekarar 2017 ne aka fara hukunta Jami’an gwamnatin APC da aka samu da laifi, wanda ya ci tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babaciri, duk da dai ana ganin matsin lamba ta ‘yan kasa ce ta sa aka hukunta Babaciri, ko da yake ba hukunta shi aka yi ba an dai cire shi ne kawai tunda har inda muke yau ba a ji shi a kotu ba ana tuhumar sa da aikata cin amana ga kasa. Amma ko ba kome dai an cireshi kuma mutane sun yarda da cewa, wannan gwamnatin zata iya taba kowa in dai an same shi da laifi duk kusancin shi da gwamnatin, wannan fili ya na fatan cewa, wannan gwamnati ta ci gaba da bibiyar baragurbin cikinta domin fitar da su, wanda hakan zai taimaka mata wajen yin ingantaccen aiki mai alfanu ga al’ummar da suka zabe ta.

Haka kuma a shekarar 2017 munana kasha-kashen kabilanci suka faru a Taraba da Adamawa, wanda a tarihi ba a taba samun irin wannan kisan da ya faru a Taraba da Adamawa ba, wanda kuma ko shakka babu laifin gwamnati ne domin ita taki inganta tsaro yadda ya kamata a yankunan har abin da ya faru ya faru, wannan fili na bayar da shawara ga gwamnati cewa, lallai ya kamata ta sani a wurinta duk yan Nijeriya baya suke komin kankantar kabila daya ta ke da kowace iri, haka kuma mutanen birni da na kauye duk daya suke, domin duk ‘yan kasa ne kuma alkawari iri daya aka dauka a kansu na kare lafiyarsu da dukiyoyin su, bai kamata ba shugabanni su rika kawar da kai ga munana ayyukan ta’addanci da ke faruwa a kauyuka ba. Domin duk hakukuwan iri daya ne.

A bangaren shari’a shekarar 2017 shekara ce da ta nuna cewa akwai gazawa a fannonin shar’ar kasar nan, domin ba wani barawon gwamnati da kotunonin kasar nan suka daure a matsayin mai laifi, sannan mafi yawan shari’o’in siyasar da kotunonin ke gabatarwa ba wadda aka zartar da hukunci sai dai jan rai da kara matsa abun gaba, wanda hakan ya tabbatar da cewa akwai matsala a kotunonin kasar nan, kuma suna bukatar gyara yadda zasu dace da adalci. Wannan fili na bayar da shawara ga gwamnati da ta yi wani gyara da zai kawo sauyi a kotunoni  kasar nan wanda zai taimakawa al’umma su fahimci cewa, za su iya samun adalci idan sun zo koto.

A kashe kuma cikin shekarar 2017 ne gwamnati tarayya ta fara biyan ma’aikatan wucin gadi na N-Powar, wanda shirin ya taimaka wajen rage zauna gari banza a kasar nan, duk da cewa shirin ya zo da matsalolin na rashin tantance wadanda suka dace da amfana da shirin, musamman yadda aka rika daukar wadanda dama cen suna aiki, amma ko ba kome dai shirin ya kayatar kuma ya taimaka sosai wajen samar da ayyukan yin a shekaru biyu kacal a wannan kasa.

Hausawa dai kan ce, “wanda ya gyara ya sani…..”

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai