An Gwabza Tsakanin Barayin Shanu Da ’Yan Sintiri A Sakkwato — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Gwabza Tsakanin Barayin Shanu Da ’Yan Sintiri A Sakkwato

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar mutum 8  a rikicin daya barke tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan sintiri a karamar hukumar Isa.

Jami’in watsa labaran rundunar, Cordelia Nwawe, ya bayyana wa manema labarai cewar, mutum 8 cikin har da wani dattijon da ‘yan bindigan suka je sacewa suka rasa rayuwarsu a hatsaniyar. Misis Nwawe ta ce, tuni aka rafa gudanar da bincike a kan lamarin, ta kuma kara da cewa, ana kyautata zaton ‘yan ta’addan sun shigo jihae sakkwaton ne daga garuruwar dake makwabtakar na jihar zamfara.

Ta kara da cewa, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya ziyarci kauyen inda ya yi ta’aziyyar ga iyalan mamatan, ta kuma tabbatar da himman rudunar ‘yansanda na ganin sun zakulo wadanda suka yi wannan mummunan aika aika da nufin kare al’uma daga aukuwar irin haka a nan gaba. Wata majiya ta labarta wa manema labarai cewa, mutum 13 ne aka kashe a sakamakon rikicin, bayan da aka katse hanzarin masu garkuwa da mutane a kokarin da suka yin a sace wani dattijo a kauyen Dan Tasango dake yankin masarautar Gebe ranar Asabar. Bayani ya nuna cewa, dattijon ya yi tirjiya ne daga kokarin sace da suka yi abin daya nan take suna dankara masa bindiga, inda nan take ya mutu.

Majiyar tamu, ta kara da bayyana cewa, hayaniyar daya biyo baya ne ya sanya ‘yan sintirin suka yi gangami inda suka bi sawun ‘yan bindigan. Amma ashe ‘yan ta’addan sun yi kwantan bauna a kan hanyar Kamarawa zuwa Bafarawa, inda ana aka yi bata kashe.

Wani da ka yi bata kashin a gabansa ya ce, ‘yan ta’adda sun kashe ‘an sintiri 7 yayin das u kuma aka kashe musu mutum 5.

“Lallai gaskiya ne ‘ya ta’adda sun rasa mutum 5 daga cikinsu, amma nan da nan suka kwashe gawarwakin kamar yadda suka saba don basa sin barin wani alamun aiyukansu na ta’addanci, inji shi.

Wani jami’in tsaro daya bukaci a sakaya sunansa, ya shawarci gwamnatocin jihohin guda biyu dasu kafa karfarfar rundunar tsaro kunshe da jami’ai daga dukkan bangarorin harkar tsaro na kasar nan domin fuskantar ‘yan ta’addan.

Advertisement
Click to comment

labarai