Emmanuel Macron Na Gab Da Samun Nasarar Shirinsa Na Sauye Sauye A Faransa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Emmanuel Macron Na Gab Da Samun Nasarar Shirinsa Na Sauye Sauye A Faransa

Published

on


Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na gab da samun nasarar shirin sa na sauye sauye ga harkokin sufurin jiragen kasa wanda ya gamu da mummunar suka daga kungiyoyin ma’aikata.

Kwamitin Majalisar kasar ta amince da matakin karshe na dokar sauya fasalin harkokin jiragen wanda zai bude kofar rage kudaden da ake kashewa da kuma bai wa masu zuba jari damar shiga a dama da su.

Yau ake saran Majalisar wakilai ta kada kuri’a a kan sauyin, yayin da gobe Alhamis kuma Majalisar Dattawa ta kada nata kuri’ar.

Minister sufuri Elizabeth Borne ta bukaci goyan bayan yan Majalisun kan shirin.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce ganawar Shugaba Donald Trump da Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un a makon gobe, za a yi ta ne a otal din Capella na Tsibirin Sentosa da ke kasar Singaore.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!