Fyade: Kotu  Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Rai Da Rai — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Fyade: Kotu  Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Rai Da Rai

Published

on


Bayan kwashe watanni 15 ana shari’a, mutumin nan Kingsley Inyang, zai karke rayuwarsa ne a gidan Yari, wannan shi ne hukuncin da babbar kotun Legas da ke zama a Igbosere, ta yanke a ranar Litinin.

An yi wa Mista Inyang daurin rai da rai ne kan yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade.

Mai shari’a Sedoten Ogunsanya, wanda ya yanke hukuncin, ya same shi da aikata laifin wanda ya saba wa sashe na 137 na kundin aikata laifuka na Jihar Legas.

Shari’ar wacce ta kwashe sama da watanni 15, Ogunsanya ya ce, masu gabatar da kara karkashin jagorancin Adebayo Haroun, sun tabbatar da laifin a kan wanda ake zargin ba tare da wata tantama ba.

Mai shari’ar ta ce, shaidar da Inyang ya bayar ba ta zo daya da wacce budurwarsa ta bayar ba, wacce ta ce, a ranar da ake zargin an aikata laifin, Inyanga ya zauna tare da ita ne na tsawon mintuna 15 kacal, inda shi kuma Inyang ya ce ai sun wuni ne tare da ita.

Inyanga, mazaunin gida mai lamba 16, da ke titin, Adetunde Arogundade, ta wajen garin Legas, an gabatar da shi ne a kotun ranar 3 ga watan Maris 2017.

A cewar masu gabatar da karan, ya yi wa yarinyar fyade ne wacce take wakiliya ce a Cocinsa, a gidansa ranar 26 ga watan Yuni 2015.

Bayan gabatar da shi a kotun a wancan karon sai ya musanta aikata laifin, aka kuma bayar da belinsa.

A lokacin da ake shari’ar, yarinyar ta ce, lokaci na farko da Inyang ya yi mata fyaden shi ne ranar wata Lahadi da Yamma, bayan sun kammala addu’a a Cocin na shi, inda kuma ya yi mata barazanar cin mata mutunci matukar ta shaida wa wani.

Bayan kwanaki uku da hakan, ni da kanina mun wuce ta kofar gidan Inyang, a hanyarmu ta komawa gida bayan mun fito daga karatun Bebul a Cocin, sai Inyang ya yafuto ni.

“Ya kori kanin nawa waje, sai ya afka mani. Ya kuma gargade ni da kar na bari wani ya ji, in ba haka ba zai bani

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!