Ghana Da Sauransu Za Su Shigo Da Mai Daga Matatar Man Dangote — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ghana Da Sauransu Za Su Shigo Da Mai Daga Matatar Man Dangote

Published

on


Kafin kaddamar da matatar mai ta Dan gote, kasashen Afrika dake shigo da mai da kuma masu rabar da man dake kasar Ghana, suna bayyana zakuwar su akan shigo da mai daga matatar man ta Dangote in ta fara gudanar da aikin ta.

Masu sayen man, sun bayyana cewar, tuni sun gama shirye-shirye don shigo da man daga babba daya tilon matatar man dake a yankin Lekki cikin jihar Lagos mallakar sannanen dan kasauwar Alhaji Aliko Dangote.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin takardar da Kamfanin rikunonin Dangote ya gabatar a ranar litinin a taron masu harkar mai na kasa da kasa na (Ghipcon) da aka gudanar a shekarar 2018, wanda ya gudana a Accra babban birnin a kasar Ghana.

Sanarwar ta kara da cewar, mahalarta taron da kuma masu rabar da man da sauran ‘yan kasuwa da suka fito daga kasashe daban-daban sun kagara su san yadda za su shiga sahun rabar da man daga ganguna 650,000 daga matatar.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya sanar da cewar, gwamnatin kasar Ghana ta sanar da cewar, tafi son ta yi hudda da matatar man ta Dangote wajen shigo da man mai makon shigo dashi daga kasuwar duniya.

Ya kara da cewa, “ yafi mana sauki mu sayi man daga matatar mai ta Dangote saboda tafi mana kusa da sauran kasashen da muke makwabtaka da su.”

Nana Akufo-Addo wanda mataimakin sa Mahamud Bawumia ya wakilce shi a wurin taron ya ci gaba da cewa, kasashen Afrika sun kagara matatar man ta Dangote ta fara aiki.

A cewar Mista Babajide Soyode, wani mai bayar da shawara akan a kamfanin na Dangote da kuma harkar mai, ya sanar da cewar, a lokacin da mataimakin shugaban kasar da ministan makamashi  na kasar Boakye Agyarko, suka kai ziyara a matatar man ta Dangote, sun yi mamaki sosai yadda suka ga aikin inda kuma suka nuna gamsuwar su akan yadda aikin yake tafiya kamar yadda ya dace.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!