Gwamna Masari Ya Ce Gwamnatinsa Za Ta Ci Gaba Da Inganta Rayuwar Al’umma — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamna Masari Ya Ce Gwamnatinsa Za Ta Ci Gaba Da Inganta Rayuwar Al’umma

Published

on


Gwamna Aminu Bello ya kara tabbatar da samar da ababen jin dadin rayuwa masu yawa ga al’ummar jihar nan.

Gwamnan na magana ne a lokacin kaddamar da rabon kayan sanyawa ga mata sama da 5,000 wadanda ake zabo daga shiyyar dan majalisar dattawa ta karamar hukumar.

Taron mai taimaka ma gwamnan ta musamman Haj Husna Aliyu ce ta shirya shi a dakin taro na Hukumar kula da ma’aikatar karamar hukumar jihar Katsina.

Gwamnan wanda ya sami wakilcin kwamishiniyyar ma’aikatar kula da harkokin mata Dr. Badiya Hassan Mashi ya ce tun hawan gwamnatin jam’iyar APC akan madafun iko mata na kan gaba sosai wajen shirin Gwamnati na kayan sana’o’in da shirin tallafin ta kara da lisafo shirin bayar bayar horon shirye-shiryen koyor da sana’o’in ga mata masu bukata ta musamman (Haka  sashen) duk na aikin shirye-shiryen.

Tun da farko mataimakawa gwamnan ta musamman Hajiya Husna Aliyu tace ta yance shawara ne ta tallafawa matan don suma su yi bikin sallah cikin jin dadi da walwala.

Hajiya Husna Aliyu ta yabawa wannan gwamnati na tallafawa mata

Ta kuma yi kira ga matan da suyi amfani da kwanakin da suka sara na azumin ramadana suyi addu’ar samun ci gaba da zaman lafiya ga jihar nan da kesa baki daya.

Sauran wadanda sukai magana a wajen sun hada da shugaba jam’iyar APC ta Katsina LG Alh. Babangida Shinkafi, shugaban mata ta shi katsina Hajiya Nasara Abubakar da Zuwaira Abubakar shugaban Mata ta APC a karamar hukumar tallafin na sallah wanda tun farko gwamnatin jihar Katsina, Katsina ta bada shi amma daga lisani sai abin ya zama cece kuce cewa wai Husuna c eta bada shi harma so kai ya shiga tsakani sai wanda aka ga dama a keba ko wanda ya iya gulma da kilbibi a ofishin ita Husnar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai