Kofin Duniya: Watakila Salah Ba Zai Bugawa Masar  Wasan Farko Ba Da Kasar Uruguay — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Kofin Duniya: Watakila Salah Ba Zai Bugawa Masar  Wasan Farko Ba Da Kasar Uruguay

Published

on


Yanzu haka ana shakkun da wuya shanararren dan wasan nan dan kasar Masar mai buga wa kungiyar Liberpool wasa, Mohammed Salah ya samu buga wa kasasrsa wasan farko a gasar wasan kwallon kafa ta Duniya da ake shirin farawa a Rasha.

Akwai babbar ayar tambaya akan ko shahararren dan wasan nan Mohamed Salah da kasar Masar mai bugawa Liberpool zai samu buga wa kasarsa wasan na cin Kofin kwallon kafa ta Duniya da za su buga tsakaninsu da kasar Uruguay a Rukuni na [A] ranar Jumu’a a can Rasha.

Wannan shakku kuwa yasamu ne saboda labarin da ke fitowa a can kasar na cewar Likitan kungiyar na kasar Masar Mohamed Abou al-Ela ya sake kwantar da shi Mohamed Salah a gadon Assibiti a ci gaba da jinyar kashin kamfalin kafadarsa da yake yi.

Idan ko hakan ta kasance, to masu sha’awar ganin wasan Mohamed Salah da dama baza su ji dadi ba, musamman lura da yanda yake taka Leda a wasanninsa, kuma wannan muhimmiyar dama ce ga Salah ya buga wa kasasrsa wasan cin Kofin Duniya kuma a rukunin farko

Mohamed salah dai zakakurin dan wasa ne da ya zura kwallaye 44 a kungiyarsa wato Liberpool a kakar wasan data gabata.

Amma mai tsaron gidan kasar Uruguay Fernando Muslera da kansa ke fatan Allah ya kaddara da Mohamed Salah ne za su buga wasan, yana cewar shi yana sha’awar ya ga kwararren dan wasa na taka leda koda yake Masar ce za ta kalubalancesu.

Advertisement
Click to comment

labarai