Majalisar Dokokin Kasar Nijar Ta Bukaci Hukumar Zabe Ta Cike Gurbin Hamma Ahmadu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Uncategorized

Majalisar Dokokin Kasar Nijar Ta Bukaci Hukumar Zabe Ta Cike Gurbin Hamma Ahmadu

Published

on


Da kuri’u takwas cikin goma sha daya ne kwamitin gudanarwa na majalisar dokokin Nijar ya amince ya aika wa hukumar zaben kasar da ta aika da wanda zai maye gurbin dan majalisa Hamma Ahmadu bayan ya yi sama da shekara biyu bai taka majalisar ba.

Shi dai Hamma Ahmadu yana gudun hijira ne a Turai sanadiyar gujewa wata shari’ar da ake yi masa a kasar wadda yake ganin wata makarkashiya ce ta siyasa.

Duk da cewa kotun kasar bata yanke shawara a kan bukatar majalisar dokokin kasa na maye gurbinsa, ‘yan adawa, musamman na kusa da shi Hamma Ahmadun, irinsu Bala Ibrahim ya dora laifin wannan al’amarin kan jam’iyyar PNDS mai mulkin kasar. Ya ce, lokacin da Hamma Ahmadu ya bar kasar bashi da lafiya. Jam’iyya mai mulki na gani Hamma ne zai zama masu kaya a zaben 2021 idan Allah ya kai rai.

Kokarin jin ta bakin ‘yan majalisar dokokin kasar ya cutura, amma mai magan da yawun jam’iyyar PNDS Adamu Manzo ya ce, an umurceshi ya jira matsayin kotun tsarin mulki kafin ya yi magana.

Sai dai kakakin PNDS Alhaji Asumana Muhammadou ya mayar da martini a kan bugun kirjin da jam’iyyar MODEN Lumana ta Hamma Ahmadu ke yin a cewa PNDS zata hadu dashi a zaben 2021. Yana tunashesu cewa a zaben da ya gabata shugaban kasa Issoufou Mahammadou ya lashe zaben da kashi 83 yayin da ya doke Hamma. A cewarsa, Hamm aba zai basu tsoro ba.

Dangane da wanda zai tsayawa jam’iyyar MODEN Lumana a zaben 2021, ‘yan jam’iyyar sun ce babu kowa sai Hamma a cewar Bala Ibrahim saboda wai sun yadda dashi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!