Masu Kafa Allunan Batsa A Kano Za Su Hadu Da Fushin Hukumar Hisba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Masu Kafa Allunan Batsa A Kano Za Su Hadu Da Fushin Hukumar Hisba

Published

on


A ranar litinin data gabata ne hukumar Hisba a Jihar Kano ta yiwa allunan talla dake dauke da Hotunan batsa dirar Mikiya a Kano, hakan na cikin manyan  ayyukan Hukumar ta hisba kan Umarni da aikin alhairi da kuma hani da  mummunan aiki.

Samamen wanda ya gudana karkashin mataimikin gwamada mai kula da aikace aikace Nasiru Isah, ya bayyana cewa hukumar Hisba ba zata zuba ido ba ta bari ana amfani da allunan Tallace Tallace a Manyan Titunan Jihar Kano ta hanyar sanyan Hotunan batsa. Saboda haka hukumar hisbar na jan kunnan duk wani Kamfani dake gudanar da harkokin kasuwancinsa a Kano da ya guji amfani da Hotonan batsa idan ko ba haka ba to zai fuskanci fushin Hukumar ta Hisba.

 

A lokacin samamen da rundunar a hisbar ta kai titin da ya zagaya Kano da kuma Titin Zaria, Hukumar tayi sa’ar ragargaza alluna guda hudu wanda ke dauke da hotunan batsa, wanda suka hada da na Kamfanin Septol da kuma Nature Secret.

Idan dai ana biye da yadda wasu kamfanoni ke  amfani wajen bayyan surar jikin mata a bayyane, wanda hakan kuma ya sabawa dokokin addinin Musulunci, kuma akwai dokoki da hukumar Hisba ta tanada ga duk mai kunnen kashin day a ci gaba yiwa wannan dokoki dibar karan mahaukaciya

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!