Ministan Shari’a Ya Shiga Tsakani A Rikicin Jami’ar NOUN Da Makarantar Lauyoyi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ministan Shari’a Ya Shiga Tsakani A Rikicin Jami’ar NOUN Da Makarantar Lauyoyi

Published

on


Kungiyar daliban Nijeriya NANS ta yaba da shiga tsakani da gwamnatin tarayya tayi a rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin Jami’ar “Open Unibersity of Nigeria (NOUN)” da Hukumar ilimin lauyoyi “Council of Legal Education (CLE).”

Kungiyar NAN ta jinjina wa Ministan Shari’a Mista Abubakar Malami a kokarin da ya yi na ganin gawnatin tarayya shigo domin samar da maslaha.

Kungiyar ta yi wannan yabon ne a sanarwar da shugaban majalisar dattijan kungiyar, Mista Taiwo Bamigbade, ya sanya wa hannu a Abuja ranar Litinin.

Malami ya yi alkawarin shiga tsakani ne don warware rikicin yayin da shugaban jami’a NOUN, Farfesa Abdalla Adamu, ya kai masa ziyara a ofishinsa.

Mista Bamgbose, ya bukaci gwamnatin tarayya ta tabatar da ta tsayu wajen ganin an warware matsalar cikin gaggawa. Ya ce, kungiyar NANS zata garkame habobin makarantar lauyouyi dake kasar nan da cibiyoyin jami’ar NOUN a duk fadin kasar nan matukar gwamnatin tarayya bata cika alkawarin da tayi ba a cikin wata uku.

“Alkawarin da gwamnatin tarayya tayi ta hannu Ministan Shari’a abin a yaba ne, haka yana nuna cewa, gwamnati na sauraron halin da jama’a ke ciki da kuma kokekokensu.

“A saboda haka muna kira ga Ministan Shari’ar ya tabbatar da cewar wannan alkawarin ba a watsar da shi a kwandon shara ba kamar sauran shawarwarin da aka yi a baya, hakan kuwa zai kara dankwafar da dalibai masu shirin zuwa makarantar lauyoyi daga samun daman ci gaba a karatunsu. ‎

“Muna fada fa karfarfar murya, cewa, kungiyar NANS ba zata ci gaba da karbar uzurin karya ba, muna kira da a gaggauta daukar dalibai da suka kamala karatun shari’a a jami’ar NOUN makarantar kwarewa na lauyoyi a cikin wannan zango da za a fara a watan Agusta na shekarar 2018 kamar dai yadda ake daukar takwarorinsu na sauran jam’o’in kasar nan”

“In har haka bai faru ba, zamu yi gangamin kulle harabobin makarantar lauyoyi dake fadin kasar nan da kuma cibiyoyin jami’ar yayin da wanna wa’adin ya kare”

Mista Bamigbade, ya kuma yi alkawarin cewa, kungiyarsu zata ci gaba da kasancewa mai bin doka da oda tare da mutunta hukumomin gwamnati matukar ana niya musu bukatunsu”

“Zamu ci gaba da yaki da rashin adalci da kuma musguna jama’a da ake yi, ba zamu zura ido muna kallo ana musgunawa daliban Nijeriya ana kuma mayar dasu abin dariya muna kallo ba tare da mun sa baki ba”

“Bukatar a nan shi ne, a dauki dukkan daliban aikin lauya na jami’ar NOUN tare da takwarorinsu na sauran jami’oin kasar nan ba tare da bata lokaci.

“Bai kamata a ce ana ci gaba da wulakanta daliban Nijeriya ba, wulakanci da wahalar da daliban aikin lauya na jami’ar NOUN suka fuskanta a ‘yan shekarun nan yana da matukar tayar da hankali, dole a kawo karshen lamarin haka” inji Bamigbade.

 

Advertisement
Click to comment

labarai