NUJ Ta Tallafa Wa Iyalan Marigayan Mambobinta Da Kayan Abinci A Kebbi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

NUJ Ta Tallafa Wa Iyalan Marigayan Mambobinta Da Kayan Abinci A Kebbi

Published

on


Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar kebbi ta tallafawa iyalan mambobin ta da suka rasu da kayan abinci da kudi ga’ yan marigaya goma shabiyar da suka rasu a cikin aikin a jihar ta kebbi a jiya.

Bukin bayar da tallafin kayan abincin da kuma tsabar kudi ga iyalan marigayan ya gudana ne a ofishin sakatariyar ta kungiyar ‘yan jarida da ke a Gesse phase One a Birnin-kebbi a jiya.

Da yake gabatar da tallafin ga daya daga cikin iyalan marigayan babban sakataren ma’aikatar watsa Labaru da kuma Al’adu ta jihar kebbi, Alhaji Shuaibu Aliero ya bayyana jindadinsa ga irin tunanin da shuwagabanin kungiyar ta NUJ a karkashin jagorancin kwamare Aliyu Jajirma su kayi na ganin cewa yadace su bada tallafi ga iyalan marigayan mambobinsu.

Babban Sakataren ya ci gaba da cewa wannan tallafin yayi daidai domin ta hakan ne kawai zainuna cewa ba’a manta da irin gudunmuwar da suka bayar da kuma sadaukar da kansu ga kasar ta hanyar aikin jarida a jihar ta kebbi da kuma kasar bakin daya.

Ya yi kira ga iyalan marigayar da suyi amfanin da tallafin kayan abinci da kuma tsabar kudin da aka basu ta hanyar da yadace. Ya kuma yi Addu’a ga marigayar da Allah ya yafe musu zunubansu kuma yabasu aljanna firdausi.

Daga karshe ya godewa kingiyar ta NUJ reshen jihar ta kebbi kanyin hakan ga iyalan mambobinta marigaya.

Shi ma a nashi jawabi Shugaban kunhiyar ta NUJ a jihar ta kebbi kwamare Aliyu Jajirma ya godewa wa gwamnatin jihar kebbi da kuma kamfanin shinkafa na Labana a jihar kebbi da irin goyon bayansu na ganin cewa wannan tallafin ya samu nasara kan cewa shugabancin kungiyar ta cimma gurin ta na ganin cewa ta tallafawa iyalan marigayan mambobin a jihar ta kebbi.

Kwamare Aliyu Jajirma ya ci gaba da cewa “iyalan marigayan sun samu tsabar kudi Naira dubu ashirin da biyar da kuma buhuhuwa shinkafa a matsayin tallafi daga kungiyar ta NUJ domin tunawa da mambobin ta a jihar ga irin kokari da kuma kwazon su a wurin aikin jarida a lokacin da suna raye”.

Haka kuma ya ce “wasu iyalan sun samu tsabar kudi Naira dubu goma da kuma buhuhuwan shinkafa a matsayin tallafin kungiyar ‘yan jarida a jihar ta kebbi.

Daga karshe shugaban kungiyar ta NUJ ta jihar, ya yi kira ga ilyalan marigayar cewa su kara hakuri kungiyar na iya kokarin ta na ganin cewa ta kula da jindadin ilyalan marigayan mambobin kungiyar ta ‘yan jarida a jihar kebbi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!