Real Madrid Ta Dauki Sabon Mai Koyarwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Dauki Sabon Mai Koyarwa

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nada Julen Lopetegui a matsayin sabon kocinta a kakar wasa mai zuwa bayan an kammala gasar cin kofin duniya.

Kungiyar ta fara neman sabon koci ne tun bayan da Zinedine Zidane ya bar kungiyar a watan da ya gabata bayan ya jagoranci kungiyar ta lashe kofin zakarun turai sau uku a jere.

Sabon kocin, mai shekara 51, ya kulla yarjejeniyar shekara uku ne da kungiyar wadda za ta fara aiki bayan kammala Gasar Cin Kofin Duniya.

Lopetegui ne zai jagoranci Sipaniya a gasar cin kofin duniya wanda ake kyautata zaton kasar tana daya daga cikin kasashen da za su iya lashe gasar da za a fara a kasar Rasha.

Lopetegui wanda tsohon kocin kungiyar Porto ne ya taba kasancewa da karamar kungiyar Real Madrid kuma sau daya ya taba yi wa babbar kungiyar wasa a matsayin mai tsaron ragar kungiyar

A karshen watan Mayu ne Zinedine Zidane ya ajiye aikin horar da Real Madrid, kwana biyar bayan ya lashe Kofin Zakarun Turai a karo na uku a jere.

Advertisement
Click to comment

labarai