Sanata Marafa Ya Tallafawa Matan Da Aka Kashe Mazansu A Zamfara Da Buhu 1,000 Na Shinkafa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sanata Marafa Ya Tallafawa Matan Da Aka Kashe Mazansu A Zamfara Da Buhu 1,000 Na Shinkafa

Published

on


Sanata Marafa Ya Tallafawa ‘Yan Gudun Hijiran Zamfara Da Buhu Dubu Na ShinkafaSanata Marafa ya bada buhu 1,000 kowane Buhu da naira 1,000 ga matan da Barayi suka kashewa mazaje a yankin zamfara ta tsakiya, jihar Zamfara.

Kafin ya ware buhu dubu sai da ya ware ‘allowance’ na kudin aiki ga mutanen da ya daura wa nauyin gabatar da wannan tallafin ga wadanan bayin Allah, Kuma ya shaidawa ‘yan kwamitin cewa yana iya yafe hakkin da ya bayar ga ‘yan siyasa idan lalurar tabawa ta farmar wadanda amanar ke hannunsu, amma bai yafe saqon da ya bayar ga Marayun da barayin Shanu suka kashe wa iyaye.

A jiya laraba 13/06/2016, sakon na sanata Kabir Garba Marafa CON, ya isa ga matan da suka rasa rayukan mazajensu, a sakamon kashin kiyashin da Barayi suka wa mazajensu a dazuzzukkan yankin da Sanata Marafa ya fito.

Al’ummar da suka samu wannan Tallafawa sun bayyana Jin dadinsu tare da ayyana Sanata Marafa a matsayin mutum mai tausayi da kuma jin takaicin halin da Mutanen yankinsa ke ciki, Wanda Kuma Allah ya bai wa damar sauke nauyin sanarwa duniya halin da Mutanen yankinsa da jiharsa ta zamfara take ciki, Wanda ta sanadiyar haka wasu marar kishin jinin tallakawa suka rataya mashi la’ada da kalmar HAUKA.

Haka kuma al’ummar yankin sun shaidi Marafa da cewa yana gaba- gaba wajen ganin yankinsa da al-ummarsa Sun samu ingantaccen zaman.

Sanata Marafa dai shi ne wakilin da duk abin da zai faru ga al-ummarsa yake kokarin tallafa masu da kuma jajanta masu da magana kan halin da suke ciki na kaka_nikayi,

Gwargwadon halin Sanata Marafa na jide nauyin da al-ummarsa suka daura mashi na wakilci.

Matan kauyukkan zamfara ta tsakiya ne Macce dubu 1000, kowace macce buhu daya da Naira dubu, N1000. Daga wakilinsu Sen. Marafa.

Malaman da aka daurawa nauyin isar da wannan tallafin sune:’

1. Liman Musa kura,
2. Liman Hassan MADA,
3. Liman zakariya Magami,
4, Malam lawali rugumawa Tsafe,
5. Liman Muhammadu Tunbido Ruwan doruwa,
6. Dattijo Alh. Ahmed Mai Aya Tsafe,
7. Malam ruwa yandoto,

Advertisement
Click to comment

labarai