Taron Girmama Abiola: Tinubu Ya Yi Wa Buhari Alkawarin Wa’adi Na Biyu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Taron Girmama Abiola: Tinubu Ya Yi Wa Buhari Alkawarin Wa’adi Na Biyu

Published

on


 

 

  • Obasanjo, IBB Da Saraki Sun

A jiya ne daya daga cikin Jagororin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya yi shelar cewa, Muhammadu Buhari ya cancanci komawa mulki a wa’adi na biyu, kuma ya sha alwashin yin iya iyawarsa wurin ganin Buhari yayi nasara a 2019.

Bola Tinubu ya bayyana wannan matsayar ta sa ne a wurin taron girmamawa da Gwamnatin tarayya ta shiryawa Abiola, Gani Fawehinmi da Babagana Kingibe. Inda aka ba Abiola lambar GCFR, su kuma sauran biyun lambar GCON

Daga cikin dalilan da Tinubun ya bayar har da batun cewa, gwamnatin Buhari ta yi kokari matuka akan wutar lantarki da kuma shirinta na ciyar da daliban makarantun Firamare. Akan haka ne, Tinubun ya ce zai zage damtse har sai Gwamnatin Buhari ta maimaita wa’adi na biyu.

Sai dai a wata sabuwa, tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi Babangida da tsoho Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ba su bayyana a wurin taron girmamawan ba.

Sai dai tsoffin shugabannin biyu sun aika da wasikar neman uzuri dangane da dalilin rashin halartarsu wannan taro na girmamawa.

Shi ma shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ba su halarci taron ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai