Turkiya Ta Kai Hari Kan Kurdawa Dake Cikin Irak — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Turkiya Ta Kai Hari Kan Kurdawa Dake Cikin Irak

Published

on


Shugaban kasar Turkiyyar Recep Tayip Erdowan ya bada sanarwar harin sojan da aka kai wa Kurdawa ‘yan aware a babban tungansu dake Iraki. Erdowan ya dauki wannan mataki ne a yayin da ya auna begen samun kuri’ar yan kishin kasa musammam a kan zaben da za a yi a wannan watan.

Tun ranar Littini ne dai aka bada labarin luguden wuta da jiragen saman yakin Turkiyya keta yi wa yankin Kandil, sai dai ba wani labarin cewa ankai hari ta kasa.

Nasarar wannan harin zai kara wa Erdowan kwarin gwuiwar fara fafitikar yakin neman zaben sa dake tangal tangal.

Kuriar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa Erdowan yana samun komawa baya, farin jininsa kuma ya na raguwa. Ga bisa dukkan alamu koda zai yi nasara to ba dai kai tsaye ba sai an tafi zagaye na biyu

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!