Yaki Da Cutar Foliyo Har Yanzu Da Sauran Rina A Kaba -Shekh Dahiru Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Yaki Da Cutar Foliyo Har Yanzu Da Sauran Rina A Kaba -Shekh Dahiru Bauchi

Published

on


Shehin Malami  Dahiru Usman Bauchi ya yi nuni da cewar har yanzu ba a gama yaki da cutar shan inna ba a kasar nan kuma ya zama wajibi iyaye da masu rikon ‘yaya dasu ci gaba da bayar da goyon bayan su don kakkabe cutar baki daya a kasar nan.

Dahiru Usman ya bayar da wannan shawarar ce a jawabin sa a lokacin bude bakin watan Ramadan da shugabannin kungiyar ‘yan Jarida masu yaki da Foliyo reshen jihar Kaduna (JAP) suka gudanar a gidan Shehin Malamin na Kaduna.

Ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a hada karfi da karfe, musamman a tsakanin iyaye wajen mika ‘yayansu masu Shekharu kasa da biyar don a yi masu allurar rigakafin cutar.

Ya sha alwashin bayar da goyon bayan sa wajen gudanar da ayyukan allurar rigakafin cutar da aka saba yi, musamman don kungiyar ta cimma nasarar yaki da cutar da kuma sauran cututtuka shida masu saurin hallaka yara a jihar baki daya.

Shekh Bauchi ya roki daukacin ‘yan Nijeriya akan kada suyi kasa a gwaiwa wajen sanar da rahoton bullar cutar a cikin gaggawa ga mahukuntan da suka dace don dakile yaduwar cutar.

Ya kuma jinjinawa shugabannin kungiyar akan tunanin su na kafa kungiyar don bayar da tasu gudunmawar wajen yakar cutar, inda ya yi kira ga sauran kungiyoyi dasu yi koyi dasu wajen inganta kiwon lafiya a kasa baki daya.

Har ila yau, a wata sabuwa kuwa, sananan malami mazaunin Kaduna, Dakta Ahmed Abubakar Gumi ya yi kira ga alummar Musulmi dasu rika amincewa da allurar ta rigakafin foliyo don bai wa lafiyar ‘yayansu kariyar data dace.

Ya bayar da wannan shawarar ce a yayin bude baki a gidan sa da kungiyar ta JAP reshen Kaduna ta shirya a gidan sa dake Kaduna, inda ya yayi nuni da cewar, allurar bata da wata illa.

Dakta Gumi wanda kwararren likita ne ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a bayar da goyon baya wajen magance dukkan cututtukan da suke yaduwa a kasar nan, musamman a tsakanin yara kanana.

Dakta Gumi ya yaba wa kokarin da hukumar kiwon lafiya ta duniya akan daukin da take bayar wa na magance foliyo da kyanda da sauran cututtukan yara, inda ya roki iyaye dasu bayar da tasu goyon bayan wajen yakar cutttukan ta hanyar mika ‘yayan su don ayi masu rigakafi.

Ya kuma yi kira ga masu juna biyu, musamman wadanda suke a karkara da su rika zuwa cibiyoyin kiwon lafiya don yin awo.

A jawabin sa tunda farko a wuraren shan ruwan biyu, Koodinatan na JAP reshen jihar Kaduna Alhaji Lawal Dogara ya sanar da cewar wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da shirya tarrrukan wayar da kan alumma da gangami da ilimantar da iyaye akan mahimmancin mika ‘ya’yan su don a yi masu allurar rigakafin cutar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!