’Yan Bindiga Sun Kona Gidaje 13 A Adamawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kona Gidaje 13 A Adamawa

Published

on


Akalla gidaje 13 ne wasu ‘yan bindigar da ake tsammanin ‘yan boko haram ne suka kone su kurmus a kauyen Kaya, kusa da garin Gulak cikin karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Rahotannin da ke fitowa daga yankin sun ce lamarin ya faru ne a shekaran jiya da safe, inda maharan da a ke zargin ‘yan boko haram ne suka kone gidajen, sai dai ba a samu rahoton asaran rayuka yayin harin ba.

Da yake magana kan batun mamba dake wakiltar karamar hukumar Madagali a majalisar dokokin jihar  Emmanuel Tsamdu, wanda kuma shine mataimakin kakakin majalisar ya ce jami’an tsaron sojoji sunyi nasaran dakile harin.

Ya ci gaba da cewa sojojin sun kashe daya daga cikin maharan inda kuma jami’in jami’an tsaron sakai guda ya samu rauni, wanda aka kwantar dashi a babban asibitin gwamnatin tarayya dake Yola FMC.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Emmanuel Tsamdu, ya tabbatar da cewa babu wani mutum ko guda da ya rasa ranshi yayin harin ‘yan bindigar, “muna yi wa Allah godiya, babu ran da muka rasa” inji Tsamdu.

Shi kuwa shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Muhammad, ya yaba da rawar da jami’an tsaron sojan suka dauka na dakeli harin ‘yan bindigar da cewa sunyi rawar gani.

Shugaban karamar hukumar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara yawan jami’an tsaron soji a yankin domin samar da tsaro, da kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Ya ce mafiya-yawan jama’ar yankin manoma ne da suka dogara ga aikin noma, rashin samar da tsaron ba kawai kwanciyar hankali za’arasa ba zai durkusar da yankin ne bakidaya.

Wannan sabon harin kone gidajen da yazo da safiyar litinin ya jefa tsoro a zukatan jama’ar yankin, cewa ko ‘yan bindigar ka’iya kawo musu wani harin na daban.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da’ake ‘yan kwanaki a gudanar da sallar Idi karama, inda bangarorin jami’an tsaro suka dauki tsauraran matakan bincike ababen hawa a Yola fadar jihar da wasu manyan garuruwa a jihar.

Jami’an tsaron sun kafa shingayen binciken ababen hawa a dukacin hanyoyin shiga fadar jihar, Mubi, Ganye da Numan jami’an tsaro ne ke bincike dauke da manyan malamai, haka kuma jirgin saman soji na shawagi a yankunan dare da rana.

Bayanai dai na cewa jami’an tsaron sun dauki matakan ne domin tabbatar da ganin anyi bukukuwan sallar idin lami-lafiya a jihar.

To sai dai akwai wasu bayanan dake nuni da cewa ‘yan kungiyar ta boko haram na shirin kai wasu manyan hare-hare kan wasu muhimman gurare a lokacin bukukuwan sallar, lamarin da ya tilasta jami’an tsaron daukan tsauraran matakan tsaro a jihar.

Cikin wata sanarwar manema labarai da kwamishinan yada labarai da tsare-tsare ta jihar Ahmad Sajoh, ya aikewa manema labarai ta shawarci jama’ar jihar da cewa bai kamata su nuna damuwa da matakan tsaron da jami’an tsaro suka dauka ba, ta ce sunyi hakan ne domin tabbatar da tsaro a lokacin sallar Idi.

Ta ce; “muna bukatar jama’a su kwantar da hankali kuma su bi doka da oda, su yiwa jami’an tsaro biyayya domin kaucema duk wani abu da zai kawo matsala” inji sanarwar.

To sai dai har kawo lokacin aiko da wannan rahoton majiyoyin jami’an tsaro a jihar sunki cewa komai kan batun.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!