Yau Za A Zabi Kasar Da Zata Karbi Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya Na Shekara Ta 2026 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Yau Za A Zabi Kasar Da Zata Karbi Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya Na Shekara Ta 2026

Published

on


A Jajiberin soma gasar cin Kofin kwallon kafa ta Duniya da za a yi a kasar Rasha ne hukumar FIFA za ta zabi ko wace kasa ce za ta sami damar karbar bakuncin gasar a shekara ta 2026 tsakanin kasashen yankin Arewacin Amurka da na yankin Arewacin Afrika.

Yanzu haka ana maganar mai yuwa ne a yau, mambobin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA su zabi wata kasa a yankin Arewacin Amurka ko kuma su zabi sake mai da gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya da za a gudanar a 2026 a wata kasa ta Afruka a karo na biyu kuma Morocco ne ake hasashe idan har an maida wasan a yankin Nahiyar Afrika.

To amma kuma abin a fili yake, ko dai a zabi yankin Arewacin Amurka da suka hada da kasashen Medico da Canada ko kuma a zabi mai fatar ganin ta samu dama wato Morocco wadda kuma filayen wasanninta bakimtsatstsu bane.

To ko ma dai miye a jajibirin wannan gasar ta 2018 ne kasashe mambobin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA za su jefa kuri’ar zaben kasar da za ta kasance mai karbar bakuncin gasar ta 2026, sai dai kasar Morocco bata fara batun neman kuri’un mambobin ba sai a farkon wannan watan, kuma ita hukumar FIFA ta yi gargadin cewar akwai kasada amincewa da kasar ta Morocco da ke a yankin Arewacin Afrika saboda rashin manyan filayen wasa da masaukan baki, da hanyoyin sufuri da dai sauransu.

Amma dai kasashen na yankin Arewacin Amurka da suka hada da Medico da Canada ne kan gaba a gasar neman damar idan aka yi la’akari da matsayin da suka samu na zama bagire mafi inganci idan aka kwatanta da kasar Morocco.

Advertisement
Click to comment

labarai