Albarkar Noma Kan Bunkasa Fitar Da Kaya Waje Daga Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Albarkar Noma Kan Bunkasa Fitar Da Kaya Waje Daga Nijeriya

Published

on


Tun da jimawa, Nijeriya ta kasance tana fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen waje, sai dai har kawo yanzun, yanda dai aka saba tun tale-talen dai hakanan ake yi ba tare da samo sabbin hanyoyi da dubaru na kara inganta harkar ta fitar da amfanin gonan waje ba, wanda hakan ya sanya ba wani mahimmin sakamako na azo a gani da ake samu. Kai hatta ma babbar hajar da muke tutiya da ita a wajen ta danyan man fetur, ita ma dai jiya-i-yau, danyan dai muke fitarwa, a tace a maido mana da shi mu saya, mun kasa ci gaba ya zamanto mune muke tace kayanmu mu kai wajen mu sayar.

Abin da hakan dai ke nufi shi ne, ba mu cin moriyar duk wadannan kayayyakin da muke samar da su asalan, amma fa sai kuma mun kai su waje an sarrafa su a kuma maido mana da su da dan karen tsada mu saya. A nan muke aikin, amma fa masu saye su sarrafa su sayar mana sune da ribar.!

Duk da kasancewar ababen da muke nomawa kamar su, Cocoa, Auduga, Gyada da kwakwan manja, sune suke rike mana da tattalin arzikinmu tun kafin ma kasarmu ta sami ‘yancin kanta, kai har ma jim kadan bayan samun ‘yancin kan nata. Amma dai su ma din hakanan a danyansu, tsabarsu muke sayarwa da al’ummar duniya da ke wajen kasar namu su, ba tare da mun iya koyon dubarun sarrafa su din ba ballanta mu mori jibinmu yadda ya dace. Sai sune ke gyara su, su tace su, su sarrafa su, su kuma maido mana da su ta wasu fuskokin na daban mu yi ruguguwar sayan su bisa farashin su mai dan karen tsadar da suka yanka mana! Duk wannan ne dalilin da ya sanya ba mu girban alfanun da ya dace a sashen amfanin gonan namu da muke hakilon nomawa da gumin mu.

Amma dai matukar muna son ganin ci gaban aikin da muke a sashen na gona, ya zama fa tilas da mu koyi dubarun sarrafa amfanin gonan namu akalla ko da ba duka ba, ya kasance wani sashe daga cikin hakan, kila ma dai dukan zai fiye mana alfanu. Da yawa daga cikin masu cinikin namu na waje, za su gwammace a ce mu ke sarrafa wa da inganta hajojin gonan namu kafin mu fitar masu da su kasuwannin na waje. Idan har da za mu iya mike wa tsaye yanda ya kamata mu aikata hakan, tabbas kasarmu za ta shiga sahun manyan kasashen duniya da suka ci suka sha suka kuma tumbatsa da arzikin amfanin gonan da suke nomawa su kuma sarrafa su sannan su fitar da su kasuwannin duniya na waje. A yau da yawa kasashen duniyan da suka zama masu iya dogaro da kansu a bisa tsayuwar su da amfanin gonan na su kadai.

Misali na kusa a nan shi ne, yadda kasar Habasha ta iya gina tattalin arzikinta kacokam kan aikin noman Coffee da take yi. Ta wannan fuskar ne muke yaba wa shirin da gwamnati ke yi na horas da manoma dubarun da za su kara wa ababen da suke nomawan armashi ta yadda za su dace da yadda ake bukatar su a kasuwannin duniya. Ra’ayin wannan jaridar ne, cewa fa lokaci ya yi da za a gyara dukkanin bambance-bambancen da ke tsakanin, nomawa, sarrafawa da kuma kai wa kasuwannin kasashen waje tun daga tushen su.

Muna kara jaddada cewa, hanyar kadai da ya kamata a bi ita ce ta, ilmantarwa da bayar da horon da ya dace ga manoman mu na karkara hanyar da ya kamata su bi wajen ingantawa da kuma sarrafa amfanin gonan da suke nomawa kafin sayar da su a kasuwannin da suke bukata. Sake wa amfanin gona siffa da fasali ta hanyar, sarrafashi, sanyaya shi, busar da shi, tace shi, sanya shi a cikin mazubi na musamman da makamantan hakan, duk yana kara wa abu armashi, wanda hakan ba yana kara kawo riba ce ba kadai, yana ma samar da tulin karin ayyukan yi ga mabukata ya kuma habaka tattalin arzikin kasa bakidaya.

A bisa kididdiga, kyautata noma yana rike da matsayin kashi 21.21 na tattalin arzikin kasarmu a lissafin shekarar 2016. Wannan shi ne matakin koli a sama da shekaru 35 da suka shude, ya kai mataki na 48.57 a shekarar 2002, sa’ilin da karancin sa ya kai mataki na 20.24 a shekarar 2014. Wannan karamin lissafin kadai ya isa ya nu na mana da za mu yi abin da ya dace a fannin na inganta amfanin gonan namu da kuwa ya iya taka mahimmiyar rawa a fannin tattalin arzikin namu.

A nan, ya kamata manoman mu na karkara su daina takaita da ganin kansu masu noma abin da za su ci kadai, su mike ne su dauki kansu a matsayin manyan ‘yan kasuwa masu sana’ar noma, ta hanyar inganta sana’ar noman na su domin bunkasa tattalin arzikin namu.

Muna bayar da shawara ga gwamnatin tarayya ta karkashin Ma’aikatar ta na albarkatun gona, da ta karfafi manoman namu na karkara ta hanyar zuba jari mai gwabi wajen horas da su dubarun inganta hajojin na su kafin su fitar da su kasuwannin duniya. A iya cewa, Nijeriya ta fito daga cikin matsin tattalin arziki, amma dai har yanzun da akwai sauran rina a kaba.

Muna ganin ya kamata gwamnati ta gano amfanin gonan da aka fi mayar da hankali a kansu, da kuma wadanda suka fi samun kasuwa a waje, sai a karfafi manoman da su kara mayar da himma a kansu, su noma su, su sarrafa su, su kuma inganta su domin shirin fitar da su waje.

Da hakan, kasarnan ba kawai tattalin arzikinta ne za ta inganta ba, za ma ta samu tabbatan dogaro da kanta da abincin da za ta ci sarai. Yin hakan, zai kara samar da ayyukan yi ga matasan kasarnan, ya kuma taimaka masu ba kawai su zama masu kwazo ba, su ma zama hazikan kansu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!