Gasar Kofin Duniya Ta 2026: FIFA Ta Zo Da Sabon Salo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Gasar Kofin Duniya Ta 2026: FIFA Ta Zo Da Sabon Salo

Published

on


Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta zo da sabon salo wajen zabar kasashen da za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2026 inda ta zabi kasashe uku su dauki nauyin gasar.

Hukumar ta amince da bai wa kasashen Amurka Kanada da kuma Medico damar karbar bakoncin gasar cin kofin duniya ta 2026 bayan kudirin da suka shigar da ya doke wanda Moroko ta gabatar.

Mambobin hukumar ta FIFA ne dai suka kada kuri’a ga bangarorin biyu inda Amurka da Medico da kuma Kanada suka samu jumullar kuri’u 134 yayinda Morocco ta samu 65.

Ana ganin gasar cin kofin duniyar ta 2026 zata kasance mafi girma da kayatarwa da aka taba fuskanta a Tarihi, inda za a samu wakilcin kasashe 48 a kuma yi karawa 80 a tsawon kwanaki 34.

Tun farko dai Morocco ce ta fara mika bukatar karbar bakoncin a 2026 wanda kuma shi ne karo na 3 da ta ke neman karbar bakoncin gasar cin kofin duniyar amma kuma daga bisani kasashen Amurkan Canada da kuma Medico suka zamo mata cikas.

Mambobin FIFA 211 daga mabanbantan kasashe ne suka yi zaman tantance kuri’un yau Laraba a Rasha yayinda Ghana ta kauracewa zaman kan abin da ta magudi.

Medico dai ta taba karbar bakoncin gasar cin kofin duniyar a 1970 da 1986 haka zalika Amurka a 1994 yayinda kuma Kanada ta karbi bangaren mata a 2015.

Akwai dai zarge-zargen cewa kasashe na biya mambobin hukumar don kada musu kuri’ar nasarar karbar gasar cin kofin duniyar kamar dai yadda ya faru a 2010 lokacin da FIFA ta amince da Rasha ta karbi gasar cin kofin duniya a 2018 ita kuma Katar ta karba a 2022.

Advertisement
Click to comment

labarai