Kofin Duniya: Rasha Ta Fara Da Kafar Dama, Saudiyya Ta Kwashi Kashinta A Hannu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Kofin Duniya: Rasha Ta Fara Da Kafar Dama, Saudiyya Ta Kwashi Kashinta A Hannu

Published

on


Kasar Rasha mai masaukin baki ta fara gasar cin kofin duniya da kafar dama bayan data doke kasar Saudi Arabia daci 5-0 a wasan farko da suka buga a gasar a jiya Alhamis.

Kafin yanzu dai akwai hasashen cewa Rashan ba lallai ta yi abin kirki a wasan ba, amma daga bisani aka samu juyawar al’amura inda suka lallasa takwarar ta su.

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci Rashan ta zura kwallaye biyu a ragar Saudi Arabia kuma Lury Gazinsky ne ya zura kwallon cikin mintuna na 12 da fara karawar a filin wasa na Luzhniki da ke babban birnin kasar wato Moscow.

Yanzu haka dai Rashan za ta fuskanci ko dai Masar ko kuma Uruguay a wasan ta na gaba na cin kofin duniyar.

Matukar dai Masar ta yi nasara kan Uruguay to ita za ta kara da Rasha haka zalika idan Uruguay ce ta yi nasara itama za ta fuskanci Rashan.

Wasan dai na yau ya samu halartar shugaban kasar Rasha, Bladimir Putin da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA baya ga mashahuran mutane.

A gobe za’a cigaba da buga wasa a ruknin na farko tsakanin kasar Masar wadda take da dan wasa Muhammad Salah da kuma kasar Uruguay.

Sai kuma wasan rukuni na biyu tsakanin Morocco da kasar Farisa wato Iran sai kuma da daddare za’a fafata wani wasa tsakanin kasar Sipaniya da Portugal wadda Cristiano Ronaldo yake jagoranta

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!