Madrid Za Ta Kai Fam Miliyan 120 Domin Sayen Hazar — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Madrid Za Ta Kai Fam Miliyan 120 Domin Sayen Hazar

Published

on


Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya tsaf domin kai tayin kudi dayakai fam miliyan 120 ga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea domin cinikin Edin Hazard.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta dade tana zawarcin dan wasan wanda kungiyar take ganin zai iya maye gurbin dan wasa Cristianao Ronaldo a kungiyar sakamakon shahararren dan wasan yafara girma saboda shekaru kuma ana rade-radin cewa zai bar Real Madrid a wannan kakar.

Hazard, mai shekaru 27 a duniya yaki amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar Chelsea tayi masa na shekaru hudu inda aka bayyana cewa dan wasan yagaji da zama a kungiyar kuma yanason ya gwada nasararsa a kungiyar Real Madrid.

Tsohon Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane ya dade yana zawarcin dan wasan tun yana mataimakin mai koyarwa a kungiyar ta Real Madrid karkashin jagorancin Carlo Ancelotti dan kasar italiya sai dai kawo yanzu shugaban kungiyar shima zai cigaba daga inda Zidane din ya tsaya duk da cewa yabar kungiyar.

Sai dai kungiyar Chelsea batason rabuwa da dan wasan nata wanda yana daya daga cikin manyan yan wasan kungiyar a daidai wannan lokaci kuma tuni mai koyar da yan wasan kungiyar, Antonio Conte ya bayyana cewa bai kamata kungiyar ta siyar da dan wasan ba indai kungiyar tanason tacigaba da lashe kofuna.

Ana saran kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata kai tayin kudi fam miliyan 120 a tayin farko domin a fara cinikin sai dai watakila dan wasan zai kai kusan fam miliyan 150 idan har Chelsea zata amince da siyar da dan wasan nata dan asalin kasar Belgium.

Advertisement
Click to comment

labarai