Gwamna Bagudu Ya Koka Kan Shigo Da Shinkafa A Kasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamna Bagudu Ya Koka Kan Shigo Da Shinkafa A Kasa

Published

on


Gwamnan jihar kebbi sanata Abubakar Atiku Bagudu ya koka kan shigo da shinkafa a kasar Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayi da yake karbar tawagar sarakunan gargajiya na jihar kebbi da suka kawo masa ziyarar gaisuwar sallah a fadar gwamnatin jihar, a lokacin da yake jawabinsa ga sarakunan a fadar to gwamnatin jihar da ke Birnin-kebbi a jiya.

Gwamnan ya ci gaba da kokawa sarakunan cewa ya lura cewa yawan shigo wa da shinkafa a kasar nan ya dawo wanda zai kawo cikas da kuma damuwa ga kamfunan casar shinkafa da kuma manoman kasar nan kan shirin bunkasa tattalin arzikin kasar nan ta hanyar noman shinkafa, Alkama da kuma sauran kayan amfanin gona a kasar nan.

Saboda haka yayi kira ga manyan sarakunan da su taimaka suyi Kira kan wannan matsala ta shigo wa da shinkafa a kasar nan yasoma zama barazana ga kamfunnan casar shinkafa da kuma manoma a jihar kebbi da kuma sauran johahin kasar nan.

Bugu da kari Gwamna Bagudu ya yabawa sarakunan kan irin rawar da suke takawa wurin ganin cewa an samu zaman lafiya jihar kebbi da kuma kasa bakin daya. Haka kuma ya gode musu ga irin goyun bayan da suke baiwa gwamnatin jihar da kuma ta tarayya kan ci gaban da aka samu a jihar kebbi da kuma kasar Najeriya baki daya.

Har ilayau, Sanata Bagudu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumomin da masu ruwa da tsaki ga harakar noma a kasar nan kan matsalar shigo wa da shinkafa a kasar nan domin magance damuwar da kamfunnan casar shinkafa da kuma manoman kasar nan ke fuskanta.

Daga karshe ya godewa sarakuman gargajiya da duk makarabansu da suka kawo ziyarar gaisuwar sallah a fadar gwamnatin jihar ta kebbi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai