Illar Zuwa Yawon Sallah Ga ’Ya’ya Mata — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Illar Zuwa Yawon Sallah Ga ’Ya’ya Mata

Published

on


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. A yau za mu yi magana ne a kan illolin zuwa yawon sallah ga ’ya’ya mata a lokacin bikin sallah a jihohin arewacin Nijeriya.

Sau da yawa Malam Bahaushe na da wasu al’adu masu kyan gaske wadanda ba su sabawa Shari’ah ba ta bangarori da dama; daga ciki su akwai yawon sallah da Bahaushe ya ke gudanar da shi sau biyu a shekara daya.

Idan za mu kalli ita wannan al’adar yawon sallah ta Malam Bahaushe za ka ga abu ne mai matukar muhimmanci, saboda wani aiki ne da ya yi daidai da Shari’ah tunda ba komai a ke kira yawon sallah ba face ziyarar dangi ko aminan arziki, don nuna farin ciki da zagayowar wata rana da ta ke zuwa sau daya a shekara, wanda da yawa idan wani ya kawo wannan rana, to wani ba zai kawo ta ba. Don haka ya sa a ke bai wa shi wannan al’adar muhimmanci daga yara har manya.

To, shin ta yaya wannan yawon sallan ya rikide ya koma wani abu daban? A lokutan baya da yawa daga cikin iyayenmu maza da mata sun ci gajiyar yawon salla ta hanyoyi da dama kamar haka:

A lokacin baya an kulla zumunci a sanadiyar ziyarar yawon sallah tsakanin dan wa da dan kani, haka zalika an kulla aure tsakanin ’ya’yan makota, kuma da dama zumuncin aure ya kullu tsakanin yaran abokai duk a sanadiyar ziyara na yawon sallah.

Kuma a wasu shiyyoyin ma a kan yi amfani da ziyarar yawon sallah wajen sulhun sabani na aure ko cinikaiyya domin wani lokacin idan sabani ya shiga tsakanin miji da mata iyaye kan cewa miji ka yi hakuri idan kun zo yawan sallah za mu tautauna matsalar, don a sami mafita. Kai, madalla da irin wannan yawon sallah na zamanin baya!

To, mene ne bambancin yawan sallar da a ke yi yanzu da na lokutan baya? Gaskiyar magana ita ce, akwai bambanci mai nisan gaske, domin kuwa shi yawan sallar da a ka yi a lokacin baya ka na iya ce ma sa halas kada’an domin na lokutan baya hada zumunci a ke yi ba bata zumunci ba.

Yawon sallar wannan lokacin rashin fa’idarsa ya fi fa’idodinsa yawa ta hanyoyi da da dama kamar haka; a yanzu batagarin samari na amfani da yawon sallan da Hausawa ke yi a wannan lokacin wajen bata tarbiyyar ’yan mata. Haka kuma batagarin ’yan mata na amfani da yawon sallar yanzu wajen cusawa kawayensu dabi’a ta banza.

Haka kuma akwai iyaye masu kwadayi da yawan sallah kan kai su tashar danasani, domin da yawan lokuta za ka ji a na jani-in-jaka a gaban alkali tsakanin iyaye bisa amfani da samari ke yi da yawon sallah su na bankawa ’yan mata ciki.

Bayan irin wannan lalatar da ke faruwa a yayin da budurwa ta je dakin saurayi neman kudin yawon sallah to yanzu lamarin ya wuce nan ma. Yanzu mafi munin abinda ke faruwa shi ne abin ya wuce kan ’yan mata da samari, ya koma kan mata masu aure da tsofaffin samarinsu na baya kafin zuwansu dakin mijinsu, domin haka kawai za ka ji amarya ta matsawa ango za ta je gidansu yawon sallah.

To, da ma angon ya auro ta da soyaryar wani saurayi a zuciyarta, wanda shaidan ke amfani da wannan damar ya ke kulla tsiya a tsakaninsu duk da ta na da igiyar aure a tsakainta da wani. Da zarar ta je gidansu yawon sallah ta kyalla ido ta gan shi, sai ka ji a na musayar lambar waya, wanda idan mijin bai sanya idanu ba sai ka ji a na artabu a gaban kuliya.

Bayan haka a yanzu lamarin yawon sallah ya kara lalacewa, domin a halin yanzu masu bata kananan yara da fyade su ma duk sun tattara komarsu sun zuba ta a kan bikin sallah.

A duk lokacin da uwargida za ta dinka wa diyarta kayan sallah, to ta kiyaye domin kamar yadda ba kowane fim ya kamata ka sanya wa yara su na kallo ba, to haka ma wajen sanya tufafi ki dinkawa diyarka kaya na mutunci, saboda yanzu akwai batagari.

Da yawan yaran da a ke tsinta a tsoffin gini an yi masu fyade bincike na nuna cewa wanda ya yi fyaden ya yi amfani da yanayi da ya ga yarinyar a ciki ko ta na da sakewa da kowa ko kuma an da sa ma ta adon an tura ta yawon sallah makwabta ga hadari ta taso kuma ga shi daga ita sai shi a lungu kuma ya shawo kwayoyi masu gusar da hankai. To, lokacin da zai aikata barnar bai sani ba ma.

Don haka bincike ya nuna cewa kusan duk shekara idan zaka ziyar ci kotuna sai ka ji a na shari’ar wani saurayi ya yi ma wata budurwa ciki daga zuwa karbar goran sallah ko kuma ka ji an ce sun je yawan salla sai hadari ya taso sun tsaya fakewa sai wani dattijo ya yi ma ta fyade ya gudu.

Ko kuma sun je yawon sallah daga nan kuma su ka ce za su je Hawan Daushe, amma sai ta biya gidan kawarta sai ta raka ta wajen saurayinta a wani gari. Yayin dawowarsu sai mota ta gagara samuwa. Hakan ya sa har sai da su ka kwana, sai washegari su ka dawo daga bisani a ka jefa ta cikin mawuyacin hali ga shi a na ganinta da mutunci a unguwarsu, ga mahaifinta shi ne limamin unguwarsu da sauransu labarai dai makamanta wadannan. Don haka ne na dora maganar zuwa yawon sallah a kasar Hausa bisa mizani kuma mun sani amsa da hankali zai ba ka cewa rashin amfaninsa ya fi amfanisa yawa.

Mu na rokon Allah ya tsare ma na yaranmu daga tsarin batagarin samari zuwa dattijan banza. Amin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!